Nan muka kawo karshen shirin
Sunana Mohammed Abdu da fatan za kuci gaba da kasancewa da mu domin kawo muku wasannin gasar cin kofin duniya kai tsaye da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Sai da safenku.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammed Abdu tare da taimakon AI
Sunana Mohammed Abdu da fatan za kuci gaba da kasancewa da mu domin kawo muku wasannin gasar cin kofin duniya kai tsaye da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Sai da safenku.
An tashi wasan, kuma sun raba maki a tsakaninsu.
Kowacce tana da maki hurhudu a rukuni na 12 daga baya wasan karshe a tantance wadanda za su kai zagayen yan 32.
Prince Adu ya fita, an kuma maye gurbinsa da mai tsaron baya, Baba Rahman.
Ingila ta kwaso kwana har sau biyu ta hannun Declane Rice, amma ba ta amfana da ita ba.
Ingila sai kara sa matsi take, amma lokaci ya kure, amma a tamaula komai zai iya faruwa.
Lokaci ya cika an yi karin minti shida kamar yadda aka yi a zangon farko.
Har yanzu dai babu ci a wasan, idan aka tashi haka sun raba maki kowanne.
Marcus Rashford ya yi fushi sosai yayin da aka ba Ghana bugun tazara, Bai yi tunanin ya aikata laifi.
O'Rilley na Ingila ne ya sawa kwallo ka, amma ta bugi turke ta kuma je wajen Kane, wanda bai kwantar da hankali ba ya dage ya buga ta sama da yawa.
Kadan ya rage Ingila ta ci kwalo ta hanun Saka ya buga da karfi amma golan Ghana ya ture.
Thomas Tuchel ya yi canji na biyar kuma na karshe.
Marcus Rashford ya maye gurbin Noni Madueke.
Wai yaya aka yi Ghana ba ta cin kwallon nan ba, Prince ne ya jawo kwallo da gudu tun daga baya ta bangaren hagu ya kuma shiga gidan Ingila, amma Konsa ya yi masa cikas ya fadi kasa bai samu buga kwallon ba, duk da haka yana kasa ya taba ta.
Harry Kane ne ya ture Sanaya, wanda ya fadi a cikin gida ya kama baya, kai kace kashin bayansa aka karya, amma dai alkalin wasa ya busa laifi.
Ƙarin canji daga Ingila.
Morgan Rogers ya maye gurbin Jude Bellingham. Eberechi Eze ya canji Elliot Anderson.
Sun koma zagaye na biyu, bayan shan ruwa.
An je hutun shan ruwa.
Daga nan su dawo a karasa zango na biyu.
Da Alama dai Ghana so take a raba maki a wasan nan, idan haka ta samu za ta amfana da maki hudu, sai ta fuskanci Croati a wasa na karshe a cikin rukuni a makon gobe.
An buga kwallo mai kyau daga bangaren hagu zuwa gidan Ghana a sama, kuma Saka ya sa kai amma ta yi yawa ta fita waje.
Nico O'Reilly da Bukayo Saka sun shiga fili, sun kuma maye gurbin Anthony Gordon da Djed Spence.
A Ghana kuwa, Abdul Fatawu da Prince Adu sun maye gurbin Inaki Williams da Jordan Ayew.