Jam’iyyar PDP tsagin Kabiru Tanimu Turaki ta tsayar da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Jam’iyyar ce ta sanar da hakan bayan ta wallafa takardar shaidar tsayawa takarar Goodluck Jonathan a babban zaɓen ƙasar na 2027.
Farida Umar, Mataimakiyar sakataren yaɗa labaran jam'iyyar PDP ɓangaren Turaki ta ƙasa ta kuma shaida wa BBC batun tsayar da Jonathan a matsayin wanda zai kara da shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Lamarin ya biyo bayan canjin wurin gudanar da taronta na ƙasa da jam’iyyar ta shirya a Abuja a yau Asabar, 30 ga watan Mayu, bayan da ‘yan sanda suka hana mambobinta shiga A Class Hotel, wurin da aka fara tanada domin gudanar da taron.
Daga bisani jam’iyyar ta sauya wurin taron cikin gaggawa, inda aka kammala shi cikin ƙanƙanin lokaci.
A wajen taron, an gabatar da matakin tsayar da Jonathan, wanda aka ce ya samu goyon bayan manyan jiga-jigan ɓangaren Turaki na jam’iyyar.
Rahotanni sun ce an mika takardar shaidar tsayawa takara ga Fred Agbedi, wanda ya karɓa a madadin tsohon shugaban ƙasar, yayin da manyan mambobi irin su Prof. Jerry Gana, Tanimu Turaki da Adolphus Wabara suka halarci taron. Jam’iyyar ta ce duk da taƙaddama da cikas, za ta ci gaba da shirinta na siyasa domin tunkarar zaɓen 2027.
Tun dai lokacin da jam'iyyar ta bayyana cewa ta tattance Jonthan har zuwa lokacin da ta tabbatar da cewa shi ta tsayar a matsayin ɗan takararta ba, ba a ji ta bakin tsohon shugaban ƙasar ba akan ko ya yarda zai sake tsayawa takara a shekarar 2027 ko a'a
Jonathan dai yayi shugabancin ƙasar daga shekarar 2010 zuwa 2015.
Shine shugaban ƙasar da aka taɓa kayarwa a kan mulki kuma ya amince da kayarwar da aka yi masa.