Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 07/09/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 07/09/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Iran ta gargaɗi Koriya ta Kudu kan atisaye a mashigar Hormuz

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baqaei, ya yi gargaɗi ga Koriya ta Kudu a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa shiga duk wani atisaye a Tekun Fasha da mashigar Hormuz zai haifar da “mummunan sakamako”.

    Ismail Baqaei ya ce a cikin wani saƙo da ya rubuta da harshen Koriya cewa, “Iran za ta ɗauki kasancewar Koriya ta Kudu a yankin a matsayin hari da kuma shiga cikin abin da ta kira ‘ta’addancin Amurka’.”

    Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da Koriya ta Kudu ke nazarin zaɓuɓɓuka daban-daban kan yadda za ta shiga ƙoƙarin tabbatar da tsaro da kuma ’yancin sufurin jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

  2. Isra'ila ta yi barazanar ƙaddamar da yaƙi kan Hukumar Falasɗinawa

    Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi barazanar ƙaddamar da yaƙi gaba ɗaya kan Hukumar Falasɗinawa idan har ta shirya kai wa Isra’ila hari irin wanda Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoban 2023.

    Mista Katz ya yi wannan furuci ne jim kaɗan bayan wani Bafalasɗine ya daba wa wani Bayahude mazaunin matsugunan Yahudawa da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, lamarin da ya jikkata shi.

    Daga bisani sojojin Isra’ila sun harbe mutumin da ake zargi da kai harin har lahira.

    A wani lamari daban kuma, an harbe wani matashi Bafalasɗine mai shekara 18 har lahira a wani ƙauye da ke Gaɓar Yamma yayin wata arangama da mazauna matsugunan Yahudawa.

    Rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta ce an tura dakarunta zuwa yankin ne domin daƙile rikicin, kuma sun buɗe wuta ne bayan da Falasɗinawa suka riƙa jifansu da duwatsu.

  3. Mijin shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ya rasu

    Mijin shugabar ƙasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, Hafidh Ameir Hassan, ya rasu a yau Litinin 7 ga Satumban 2026.

    A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ƙasar Tanzania, Deogratius Ndejembi, ya fitar a yau, ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne yayin da yake jinya a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar.

    Sanarwar ta ce Hafidh na karɓar magani ne sakamakon wata matsalar da ke da alaƙa da zuciya, kuma ya rasu da misalin ƙarfe 8:00 na safe.

    ''Tuni ake ci gaba da shirye-shiryen jana'izarsa a yankin Kizimkazi da ke Zanzibar'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

  4. Qatar: Ƙawance da Amurka abu ne mai kyau, amma shi kaɗai bai wadatar ba

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar ya ce dangane da tsaro da kariyar ƙasar, wajibi ne ƙasashen yankin Tekun Fasha su fahimci cewa kasancewa da kawancen dabaru da Amurka abu ne mai kyau, amma shi kaɗai ba zai wadatar ba.

    Majid Ansari ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya ce ƙasashe na iya samun abokan hulɗa ko ƙawayen yaƙi, amma idan aka zo batun tsaro, dole ne su dogara da kansu.

    "Dogaro da kai wajen tabbatar da tsaro shi ne kaɗai hanyar da za a bi a gaba," in ji shi.

    Jami'in na Qatar ya yi wannan bayani ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsaron yankin da kuma tasirin rikice-rikicen da ke shafar kayayyakin makamashi.

    Iran dai ta sha kai hare-hare kan wasu cibiyoyin man fetur da iskar gas na Qatar tun bayan fara rikicin da ya biyo bayan harin da Amurka da Isra'ila suka kai, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

    A ɗaya daga cikin hare-haren, Iran ta kai hari kan wata babbar cibiyar fitar da iskar gas da aka sarrafa zuwa ruwa (LNG) a Qatar, a matsayin martani ga hare-haren da aka kai kan cibiyoyin man fetur nata.

    Lamarin ya ƙara tayar da hankalin masu sa ido kan batutuwan makamashi, saboda fargabar cewa rikicin na iya yin tasiri ga samar da makamashi a duniya.

  5. 'Za mu mayar da martani idan IAEA ya kai batun nukiliyarmu gaban Kwamitin tsaro na MDD'

    Dangane da sabon daftarin ƙuduri da ƙasashen Turai suka gabatar a Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), wanda ka iya kai batun shirin nukiliyar Iran gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baghaei, ya ce idan aka amince da ƙudurin, Iran za ta ɗauki matakan mayar da martani.

    Da yake mayar da martani kan wannan ƙuduri, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce da alama ƙasashen Turai ne ke komawa ga batun shirin nukiliyar Iran a duk lokacin da suka kasa cimma muradunsu a wasu fannoni.

    Ya kuma ce a wani lokaci ma babban daraktan Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) kan jefa kansa cikin suka domin ƙara matsin lamba na siyasa kan Iran.

    Baghaei ya ce wannan mataki ya ƙara tabbatar da hujjar da Iran da China da Rasha ke yi na cewa tsarin dawo da takunkumai, wanda aka fi sani da "snapback", haramtacce ne kuma ba za a iya aiwatar da shi ba.

    Ya bayyana shirya wannan daftarin ƙuduri a matsayin "maimaita wata hanya mai cutarwa", yana mai cewa ƙasashen Turai uku sun koma gefe kuma ba su da wani tasiri sosai a batun shirin nukiliyar Iran.

    Baghaei ya jaddada cewa hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran sun haifar da cikas ga ayyukan hukumar IAEA, lamarin da ya sa a halin yanzu ba zai yiwu a gudanar da binciken cibiyoyin ba.

    A gefe guda kuma, ƙasashen Turai da hukumar IAEA na son a ci gaba da gudanar da bincike a cibiyoyin nukiliya, musamman waɗanda aka kai wa hari.

    Baghaei ya yi gargaɗin cewa idan kwamitin gudanarwa na hukumar IAEA ya amince da ƙudurin, Iran za ta ɗauki matakan ramuwar gayya domin mayar da martani ga matakin.

  6. 'Iran ta fara amfani da makamin da ta ƙera musamman don farmakar jiragen Amurka'

    Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron ta Iran, Mohsen Rezaei, ya ce Iran ta fara amfani da wani makami mai linzami da ta ƙera da kanta domin tunkarar jiragen ruwan yaƙi na Amurka.

    A wata hira da ya yi ta talabijin, Rezaei ya ce "Cikin sa'o'i 48 da suka gabata, mun gwada a karon farko wani makami mai linzami na Iran da aka ƙera domin yaƙar jiragen ruwan yaƙi. Wani jirgin ruwan Amurka ya kai masa hari, amma wannan makamin ya jefa Amurka cikin damuwa, har ta kai ga tilasta musu janyewa."

    Sai dai rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ba ta mayar da martani kai tsaye kan wannan iƙirari na Iran ba.

    Amma a wata sanarwa da rundunar ta wallafa a dandalin X a jiya lahadi, wadda ake ganin tana nuni da wani hari da aka kai wa jiragen ruwanta biyu, ta ce "saƙonmu ga dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran a bayyane yake''.

    ''Idan kuka kai hari kan jiragen ruwanmu biyu, za mu ƙaƙaba ƙarin tsauraran takunkuman tattalin arziki kuma mu lalata uku daga cikin jiragen ruwanku."

    Sanarwar ta ƙara da cewa Amurka ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare dakarunta ba.

    ''Kuma idan ya zama dole, za mu lalata wasu daga cikin tankokin dakon man fetur na Iran idan suka tsinci kansu a cikin yanayi mai rauni."

    Mohsen Rezaei, wanda tsohon kwamandan dakarun juyin juya halin Iran ne, ya kuma yi magana kan irin ƙalubalen da jiragen ruwa masu dakon kaya da ke aiki a yankin za su iya fuskanta.

    "Duk wani jirgin ruwa da ya karya sharuɗɗan da aka gindaya, kuma ya yi aiki a yankin ba tare da tuntuɓar Iran ba, za a sanya shi cikin jerin takunkuman Iran. Haka kuma zai iya fuskantar wasu matsaloli, ciki har da wahalar zirga-zirga a yankin nan gaba."

  7. Jirgin yaƙin Amurka na USS Ross ya isa Kenya bayan yaƙin Iran

    Wani jirgin ruwan yaƙin Amurka mai ɗauke da makamai masu linzami, USS Ross, ya isa tashar jiragen ruwa ta Mombasa a wata ziyara da aka tsara tun da farko, yayin da Amurka da Kenya ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarsu kan tsaron teku da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

    Jirgin yakin na USS Ross, wanda ke cikin rukunin jiragen ruwa na Arleigh Burke-class, ya isa Mombasa ne a ƙarshen mako, a yayin wani aiki da rundunar sojin ruwan Amurka ke gudanarwa a yankunan Afirka da Turai.

    Muƙaddashiyar Jakadiyar Amurka a Kenya, Susan M. Burns, ta ce ziyarar na nuna irin ƙarfin dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    ''Wannan ziyara ta nuna ƙarfin haɗin gwiwar Amurka da Kenya da kuma dogon tarihin da muke da shi na aiki tare kan batutuwan yankin da suke da muhimmanci ga ɓangarorin biyu," in ji Mrs Burns.

    Ta ƙara da cewa tasoshin jiragen ruwa na yankin kamar ta Mombasa na bai wa sojojin Amurka damar samun muhimman ayyuka kamar samar da kayayyaki da man fetur da sauran abubuwan da suke buƙata, yayin da irin waɗannan ziyarce-ziyarcen jiragen ruwa ke taimakawa wajen musayar ƙwarewa tsakanin dakarun Amurka da na Kenya.

    Kwamandar jirgin na USS Ross, Kyaftin Pia Chapman, ta ce ziyarar ta kuma bai wa sojojin da ke cikin jirgin damar hutawa bayan wani lokaci da suka shafe suna yaƙi da Iran.

    "Dakarunmu sun yi aiki tuƙuru matuƙa a yayin wannan aiki, inda suka gudanar da ayyukansu cikin tsari da ƙwarewa da haɗin kai," in ji Chapman.

  8. Mutum biyar sun mutu bayan jirgi ya yi hatsari a Amurka

    Wani jirgin dakon kaya na kamfanin Amazon Air ya kauce daga titin saukar jiragen sama yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jiragen sama na Miami International Airport, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyar tare da jikkata wasu biyar da munanan raunuka.

    Jirgin dakon kayan ƙirar Boeing 767-300 ya yi hatsarin ne jim kaɗan kafin ƙarfe biyu na rana agogon ƙasar (19:00 agogon GMT), bayan da ya tashi daga filin jirgin sama na Luis Muñoz Marín da ke San Juan, Puerto Rico.

    Har ila yau, jirgin ya bugi wasu motoci da ke kusa da wurin da hatsarin ya auku.

    Kamfanin Amazon ya ce yana "aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomi da sauran jami'an da abin ya shafa domin gano ainihin abin da ya faru."

    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka (FAA) ta dakatar da duk wani tashin da saukar jirage a filin jirgin saman, yayin da jami'an kashe gobara da na agajin gaggawa suka garzaya wurin da hatsarin ya faru.

    Hatsarin ya afku ne a daidai lokacin hutun Ranar Ma'aikata - ɗaya daga cikin lokutan tafiye-tafiye mafi yawan cunkoso a shekara.

    Magajin garin gundumar Miami-Dade, Daniella Levine Cava, ta bayyana a wani taron manema labarai da yammacin ranar Lahadi cewa, "Aƙalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka jikkata."

  9. Yaƙinmu da Rasha zai iya ci gaba har zuwa lokacin hunturu - Zelensky

    Volodymyr Zelensky ya ce yana sa ran ci za a ci gaba da gwabza yaƙi da Rasha har cikin lokacin hunturu.

    Ya bayyana haka bayan tattaunawarsa ta farko da jakadun Donald Trump a Kyiv-Jared Kushner da Steve witkoff.

    ''A yanzu mutane da dama a nan na shiryawa don tsananin da wannan rikici zai yi da kuma tsananin faɗa a lokacin hunturu,'' in ji shi.

    Amurkawan sun fara tattaunawa ta biyu da Shugaban Ukraine bayan sun yiwa ƙasashen ƙawance ƙarin haske.

    Mista Zelensky ya jaddada buƙatar ƙulla yarjejeniyar sulhun da ba za ta bai wa Rasha damar sake kai wani hari ba.

  10. Iran ta ce za ta sanar da sabon yankin tsaro a mashigar Hormuz

    Babban jami'in tsaron Iran, Mohsen Rezaei, ya ce Iran za ta sanar da sabon yankin da aka sanya wa tsaro a wajen mashigin Hormuz.

    Ya ce yankin zai kai har zuwa wasu sassan Tekun Fasha.

    Duk jirgin ruwan da ya shiga yankin da nufin ketare mashigin ruwan, za a saka shi cikin jerin wadanda aka sanyawa takunkumi.

    Tun da farko, mai shiga tsakani na Iran Mohammad Ghalibaf, ya yi gargadin cewa Iran za ta dauki matakin mayar da martani mai tsanani cikin kan Amurka cikin gaggawa.

  11. Sallama

    Assalamu alaikum, masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu d asafiyar wannan rana da Litinin, Mande tushen aiki ko da nasara na tsoronka, kamar yadda Hausawa ke yi wa kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.