Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Litinin 14/09/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Mayaƙan Houthi sun sake kai hare-hare kan cibiyoyin soji a Saudiyya

    Ƴan tawayen Houthi na Yemen sun sake kai hare-hare kan cibiyoyin soja a Saudiyya ta amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a ranar Litinin.

    Houthi sun ce sun harba jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami da dama zuwa cikin ƙasar Saudiyya.

    Bayan hare-haren, hukumomin kare fararen hula na Saudiyya sun fitar da gajeren gargaɗi ga mazauna biranen Khamis Mushait da Abha, waɗanda ke kusa da iyakar Yemen.

    A baya-bayan nan ne Houthi suka ƙwace iko da gaɓar Tekun Maliya da kuma mashigar ruwan Bab al-Mandab.

    Muhimmancin wannan hanyar ruwa ya ƙaru sakamakon matsalolin da suka addabi zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz a lokacin yaƙin Amurka da Iran.

    Wani mazaunin birnin Khamis Mushait a Saudiyya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya ji "manyan ƙarar fashe-fashe" waɗanda suka haddasa gobara da ta ci gaba da ƙonewa "na dogon lokaci".

    "Ko kaɗan ba mu samu damar yin barci ba," in ji shi.

  2. NDLEA ta kama muggan kwayoyin Colorado a Lagos

    Hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta sanar da kama wata nau'in tabbar wiwi da ake kira Colarado a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad da ke birnin Lagos. Hukumar ta ce nauyin ta ya kai sama da sama da kilogram 27, da aka boye a cikin wani jirgin daukar kaya da ya fito daga kasar Birtaniya.

    Sun kuma kama wani da ake alakantawa da kayan mai suna Abidin Jide Salami, da ya zo daukar kayan a madadin dan uwansa da ke can Birtaniya, ta amfani da wata lambar sirri. NDLEA ta kuma kama kunshi biyu na Colorado da aka boye a cikin kayan kade-kade mai nauyin sama da kilogiram 44, a wata tashar mota a birnin Lagos din, sun kuma yi nasarar cafke akalla mutum 6 da ake zargi.

    Jami'in hulda da jama'a na hukumar NDLEA, Mista Femi Baba Femi, ya tabbatarwa da BBC kamen muggan kayan mayen da wadanda ake zargi.

  3. Jami'ai a birnin Gaza sun yi gargadin fannin lafiyar yankin na gab da rushewa, sakamakon dakatar da sufurin da jami'an lafiya ke amfani da su. Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce karancin man fetur, da man juye da kayayyakin gyaran mota na daga cikin dalilan da suke hana yawancin likitoci da malaman jinya gagara zuwa zuwa aiki asibiti.

    Ma'aikatan asibiti sun ce yawanci gidajensu na da nisa daga asibitocin da suke aiki, wadanda gidajensu ke kusa kuma yaki ya daidaita su dole suke zaune a wurare mai nisa.

    Tun bayan fara yaki tsakanin Hamas da Isra'ila a shekarar 2023, fannin lafiya a zirin Gaza ke cikin mawuyacin hali, sakamakon yawan wadanda hare-hare ke jikkatawa da rasa rayuka.

  4. Ku yi nazarin alƙawuran jam'iyyu kafin zaɓar dantakara - Sutan

    Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga ƴan ƙasar su yi kyakkyawan nazari kan alƙawuran da ƴantakara suka yi musu, kafin su zaɓi wanda suke so ya wakilce su a babban zaɓen ƙasar da ke tafe na 2027.

    Sarkin Musulmi ya kuma gargaɗi ƴansiyasa kan matalar tsaro da sauran ƙalubalan da ake fama da su a gangamin yaƙin neman zaɓe, da kiran su mai da hankali kan batutuwan da za su wanzar da zaman lafiya da haɗin kai da cigaban ƙasa.

    Ya dai yi kalaman ne a lokacin da ya karɓi bakuncin kwamitin neman zaɓe na jam'iyyar APC mai mulki, ƙarƙashin jagorancin babban daraktan yaƙin neman zaɓen shugaba ƙasa, Sanata Abdul-Aziz Yari Abubakar, a fadarsa da ke Sakkwato.

    A ƙarshe Sarkin Musulmin ya yi wa kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC fatan alkhairi, da addu'ar zaman lafiya da tsaro a ɗaukacin Najeriya.

  5. An kashe matafiya 9 a harin ƴanbindiga a Filato

    Rahotanni daga jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya na cewa mutum 15 sun rasu a hare-hare daban-daban da ƴanbindiga suka kai kudancin birnin Jos.

    A ranar Lahadi ne ƴanbindiga su ka kai hari yankunan Mangu da Riyom, lamarin ya rutsa da wasu matafiya.

    Tara daga cikin mutanen fasinjoji ne da ke kan hanyar zuwa birnin Jos, da ƴanbindigar suka buɗe musu wuta a ƙauyen Dungus.

    Sai kuma sauran 6 suka gamu da ajalinsu a Mangu da Riyom, kamar yadda shugaban ƙungiyar matasan Riyom, Barista Dalyop Solomon Montrey ya shaida wa BBC.

    ''Da daddare ƴanbindigar suka kai harin, a kan babbar hanyar zuwa Abuja idan an wuce garin Mararrabar Jama'a, sun fara kashe direban motar da wasu mutane amma daga baya adadin waɗanda suka rasu ya kai 9 a wurin. Akwai matanƙkabilar Birom da Hausawa da suka fito daga kasuwa akwai kuma yara. Ƴanbindigar sun kai hari ƙaramar hukumar Mangu sun kashe mutum 2, suka dangana da Riyom tare da hallaka mata biyu wanda ba ma ayi jana'izarsu ba.''

    Jihar Filato na fama da matsalar tsaro da rikice-rikicen addini da ƙabilanci, da ke janyo hasarar rayuka da dukiyar jama'a.

  6. Ghana ta cafke masu alaka da hodar iblis da aka kama a Faransa

    Hukumomi a kasar Ghana sun sanar da kama mutum uku da ake zargi, bayan cafke kusan tan 3.9 na hodar iblis da darajarsu ta kai sama da dala miliyan 260 a kasar Faransa, da aka boye cikin tarkacen robobi daga Ghana.

    Hukumar da ke sa ido kan fataucin muggan kwayoyi ta Ghana, ta ce wadanda ake zargin su ke kula da harkar a kasar a madadin wani mai suna Jos Leijdekkers, da aka fi sani da sunan ‘‘Bolle Jos'' da ke zaune a kasar waje.

    Hukumar ta ce ana gudanar da binciken mutanen domin sanin karin mutanen da suke safarar muggan kwayoyi a kasar. Leijdekkers na daya daga cikin dillalin hodar iblis da hukumomi a Turai ke nema ruwa a jallo, bayan yanke masa hukuncin zaman kason shekaru 24 alhalin baya kotun.

    An yi amanna ya na zaune a kasar Saliyo, ko da yake gwamnatin kasar ta ce ba ta da masaniya kan inda ya ke. A bangare guda kuma babbar jam'iyyar adawa a Ghana NPP, ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kan shi kan hodar iblis da aka kama a baya-bayan nan, inda suka ce wadda aka kama a kasar a shekarar da ta gabata ta kai darajar dala biliyan daya.

  7. Kungiyar OLA a Habasha ta gargadi kamfanonin hakar ma'adinai a Oromia

    Wata ƙungiya masu ɗauke da makami a yankin Oromia na ƙasar Habasha ta yi barazana ga kamfanonin haƙar ma'adinai da ke aiki a yankin, tare da fitar da sabbin jerin buƙatu da dole su cika idan suna son ci gaba da aikinsu.

    Kungiyar Oromo Liberation Army (OLA), wadda gwamnatin Addis Ababa ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci tun kusan shekaru goma da suka gabata, tana son dukkan kamfanonin haƙar ma'adinai su riƙa ɗaukar ma'aikata daga yankunan da suke aiki.

    Sannan su bi ka'idojin kare muhalli domin tabbatar da ɗorewar ayyukan haƙar ma'adinai. Yankin Oromia shi ne mafi yawan al'umma a Habasha, kuma yana da manyan wuraren hakar ma'adanan zinari. Wannan wa'adin da ƙungiyar ta bayar na zuwa ne makonni kaɗan bayan da aka kashe mutane da dama a wani hari da aka kai a wani wurin haƙar ma'adinai a yammacin yankin.

  8. An yi jana'izar yara 26 a DR Congo

    An gudanar da jana'izar yaran da suka rasu a gobarar da ta faru a wata makaranta a yammacin Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo a makon da ya wuce. Akalla yara 26 ne gobarar ta rutsa da su a ranar Alhamis din makon jiya, a lokacin da suke daukar karatu a Bukavu. Birnin dai na karkashin ikon 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda, kuma yawancin yaran sun gamu da ajalinsu yayin da suke kokawar fita daga ajin lokacin da gobarar ta tashi. Kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa ta ba.

  9. An gargaɗi ƴan Zambiya kan cin mushen dabbobi sakamakon cutar anthrax

    Hukumomi a Zambiya sun gargaɗi ƴan ƙasar da su guji cin naman dabbobin daji bayan da dabbobi da dama suka mutu sakamakon cutar anthrax.

    Wani jami'i na hukumar kare afkuwar bala'i ya ce a ƙarshen makon da ya gabata, mutum 12 ne suka kamu da cutar bayan da suka ci naman dabbobin a yankin kogin Munyamadzi.

    Jami'in ya yi kira ga jama'a da su guji cin naman dabbobin da ba a tantance dalilin mutuwarsu ba.

    Zuwa yanzu jami'ai ba su tantance girman ɓarkewar cutar a baya-bayan nan ba inda ake ci gaba da sa ido da kuma gwaji a ɗakin gwaje-gwaje.

    A shekarar 2023, ƙasar ta yi fama da ɓarkewar cutar da ba a yi tunani ba, har ta kai mutum huɗu sun mutu sannan kuma ta bazu zuwa larduna tara cikin 10.

  10. Sojoji sun gano lita 10,000 na mai da aka 'tace ta haramtacciyar hanya' a Rivers

    Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta ce ta bankaɗo wani wajen ajiyar albarkatun mai ɗauke da lita 10,000 na man da ake zargin an tace ta haramtacciyar hanya.

    Cikin wata sanarwa ta Daraktan Yada labarai na rundunar, Abiodun Folorunsho, an yi bankaɗar ce a samamen da dakaru suka kai a ranar Asabar don daƙile satar ɗanyen mai a yankin Eleme Express na jihar Rivers.

    Ana zargin an samo man ne daga wani waje nesa da yankin wanda kuma aka ajiye domin sayarwa mutane.

    Rundunar ta ce an gano man cikin jarkoki 400 wadda kowace jarka ke ɗauke da mai lita 25 a ciki sai dai kuma babu wata haramtacciyar matata da aka gano a wajen.

    A cewar rundunar, baya ga bankaɗar, dakaru sun yi nasarar tarwatsa wata muhimmiyar cibiya ta samar da mai ta ɓarauniyar hanya.

    Sanarwar ta ƙara da cewa jami'an ba su samu cafke kowa ba kasacewar masu hada-hada a cibiyar sun tsere a lokacin da sojoji suka yi dirar mikiya a wajen.

  11. Yadda za ku sayi hannun jari

    A ranar Litinin ɗin nan ne matatar Ɗangote ta fara sayar da hannun jarin da ta ce za ta sayar ga al'ummar Najeriya domin bai wa duk wani ɗan ƙasar damar mallakar wani kaso a kamfanin.

    Kamfanin wanda zai sayar da hannayen jari guda biliyan 4.1 a kan farashin naira 525 kowane hannu, za a rufe sayarwar ne a ranar 13 ga watan Oktoban 2026.

    Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sanar da cewa matatar man fetur ɗin nasa za ta fara sayar da hannayen jari ga jama'a ta hanyar Initial Public Offering (IPO), inda aka tsara bai wa kowa damar mallakar kaso a cikin kamfanin ko da da ƙaramin jari ne.

    Wannan cigaba ne da ya buɗe sabuwar tattaunawa kan muhimmancin kasuwar hannun jari da kuma damar da take samarwa ga matasa masu son gina makoma mai ɗorewa.

    Hakan ya sa ƴan Najeriya ke yin tambayoyi dangane da hanyoyin da ya kamata su bi domin sayen hannun jari a duk lokacin da irin wannan dama ta bujuro musu ba ma lallai a matatar Ɗangote kaɗai ba.

    Da yake sharhi kan wannan dama, Dr Salihu Lukman, Mataimakin Farfesa a University of Hafr Al Batin da ke ƙasar Saudiyya, ya ce kasuwar hannun jari na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen tara dukiya cikin tsari da kuma dogon lokaci.

    Ku latsa nan domin samun bayani kan hanyoyin da ake bi don sayen hannun jari da ma samun ƙarin bayani.

  12. Hatsarin mota ya halaka aƙalla mutum 21 a Afirka ta Kudu

    Wani hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 21 a Lardin Western Cape da ke Afirka ta Kudu.

    Jami'ai sun ce mutane da dama sun ji rauni a hatsarin da ya afku kusa da garin Prince Albert mai nisan kusan kilomita 300 daga Cape Town.

    Hukumomin Lardin sun rufe babbar hanyar lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa.

  13. Saudiyya ce ta nemi a soke tattaunawar Oman - Iran

    Kakakin ma'aikatar harkokin Iran Esmail Baghaei ya ce an soke tattaunawar a aka tsara yi a Oman tsakanin Iran ɗin da wasu ƙasashen Gulf bisa buƙatar da Saudiyya ta nema.

    Wannan wata dama ce da aka bai wa Iran da Oman kuma ana sa rai cewa ƙasashen yankin za su ci moriya da kuma una godiya ga hakan, kamar yadda Baghaei ya shaida.

    Ministocin harkokin wajen Iran da Oman sun sanar da soke tattaunawar a daren jiya kuma zuwa yanzu ba a sanar da ranar da za a yi tattaunawar ba.

    Sanarwar soke taron dai ta sa farashin ɗanyen mai ya zarce dala 108 kan kowace ganga guda.

  14. Iran ta kakkaɓo jirgi mara matuƙi a Mashigar Hormuz

    Rundunar Juyin juya halin Iran ta ce ta harbo wani jirgi mara matuƙi a Mashigar Hormuz.

    Kamfanin dillancin labarai na IRIB ya ruwaito cewa dakarun IRGC ne suka kakkaɓo jirgin na MQ-1 a Mashigar ta Hormuz.

    Kakakin rundunar ya ce sabon makaman tsaron sararin samaniyar IRGC ne suka harbo jirgin ruwan tare da lalata shi.

    Zuwa yanzu IRGC ba ta yi ƙarin bayani game da batun ba.

  15. Boko Haram ta lalata aƙalla makarantu 5000 a Borno - Zulum

    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce Boko Haram ta lalata gine-ginen makarantu aƙalla 5,000, lamarin da ya sa yara miliyan 2.2 ba sa zuwa makaranta a lokacin da rikicin ta'addanci ya yi ƙamari.

    Gwamna Zulum ya bayyana waɗannan alƙaluma ne a lokacin ƙaddamar da wasu ayyuka a Maiduguri, jiya Lahadi.

    Kakakin gwamnan, Malam Dauda Iliya, ya shaida wa BBC cewa gwamna Zulum ya duƙufa wajen ganin an shawo kan matsalar tsaron tare da inganta fannin ilimi ganin irin girman ɓarnar da Boko Haram ta yi wa ɓangaren.

    A cewar kakakin, gwamnan ya gina azuzuwa kusan 5000 da gina wasu makarantu 129 sannan kuma ana sa ran kammala wasu 140 daga nan zuwa ƙarshen mulkinsa.

    Ya ce akwai yara sama da miliyan ɗaya da dubu 800 da suke makaranta saɓanin lokacin da gwamna Zulum ya karɓi mulki inda a lokacin yara dubu 800 ne kaɗai suke zuwa makaranta.

    Gwamna Zulum ya bayyana cewa Boko Haram ta kashe malamai da jami'an kula da makarantu da dama musamman a lokacin da yaƙin ya yi ƙamari.

    Zulum ya ce gwamnatinsa ta ware dala miliyan 35 a tsakanin shekarar 2025 da 2026 don inganta ilimin pramare da sakandare.

  16. 'Za a yi makonni kafin tantance waɗanda gobarar jirgin ruwan Philippine ta shafa'

    Hukumomi a Philippine sun ce za a iya ɗaukan makonni ko ma watanni kafin tantance mutanen da gobarar jirgin ruwa ta shafa a makon da ya gabata.

    Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar mutum 76.

    "Akasarinsu sun ƙone sosai," in ji Richard Allan Mangalip, wani ƙwararren jami'in bincike a hukumar ƴansandan Philippine.

    An nemi iyalan mutanen da su taimaka wajen tantance su ta hanyar gwajin DNA da kuma wasu kayayyaki da suka mallaka.

    Jirgin ruwan ƙirar MV June Aster ya nufi Coron ne daga Manila a Lardin Palawan, wani fitaccen wajen zuwa hutu, a lokacin da gobarar ta tashi ta inda ake ajiye kaya sannan kuma ta yaɗu zuwa sassan jirgin.

    Mutum 43 ne suka tsira yayin da wasu 13 kuma har yanzu ba a san inda suke ba, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

    Jami'in ya ce suna ta ƙoƙarin abubuwan da za su taya su tantance mutanen sai dai a cewar shi zai yi wuya a iya bayar da wa'adi na tsawon lokacin da za a ɗauka na tantancewar - "zai iya kai wa makonni, ko ma watanni".

    Wani jami'in tsaron teku, a ranar Asabar, ya ce abin da suka bai wa muhimmanci a yanzu shi ne tantance mutanen da kuma gano musabbabin gobarar.

  17. Farashin mai ya ɗaga a duniya bayan soke tattaunawar Iran da wasu ƙasashen Gulf

    Farashin man fetur ya sake tashi a kasuwannin duniya bayan rufe wani bututun mai mai muhimmanci a Saudiyya, da gazawar tattaunawar diflomasiyya da kuma hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a yankin Gulf.

    Farashin ɗanyen man Brent ya kai dala 108 kan kowacce ganga.

    A ranar Juma'ar da ta gabata, Saudiyya ta sanar da cewa ta rufe bututun man, bayan wasu hare-hare da Iraqi ta kai da jiragen marasa matuƙa, sun yi masa ɓarna.

    Tun da farko masarautar Saudiyya ta zargi mayaƙan ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran da kai irin waɗannan hare-hare.

    A ɓangare guda kuma, ƙasar Oman ta ɗage wani taro da aka shirya yi a ranar Litinin tsakanin Iran da ƙasashen Larabawan da ke yankin Gulf domin tattauna batun mashigar Hormuz. Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya.

  18. An fara sayar da hannun jari mafi girma na matatar Dangote

    An buɗe hannun jari mafi girma a Afirka ga jama'ar da ke da sha'awar siyan hannun jari a matatar mai ta Dangote.

    Matatar ta Ɗangote tana tayin sama da hannun jari biliyan huɗu a ƙarƙashin wata yarjejeniya da ake sa ran za ta samar da kusan dala biliyan 1.6.

    Matatar ta ƙara da cewa tana son bai wa jama'a damar kasancewa masu hannun jari a matatarsa da ta soma aiki shekaru biyu da suka gabata kuma tuni ta kasance matata mafi girma a nahiyar Afirka.

    Dangote ya bayyana cewa yana shirye-shiryen faɗaɗa aiki a matatar da za a kashe dala biliyan 14 wanda zai ruɓanya ayyukan matatar nan da shekarar 2029.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin fetur ya kusa kaiwa naira 1,400 kan kowace lita zuwa ƙarshen watan Agusta a Najeriya.

  19. 'Ya kamata NATO ta kakkaɓo jiragen Rasha a sararin samaniyar Ukraine'

    Wata cibiyar bincike da ke Amurka ta ce ya kamata ƙungiyar tsaro ta NATO ta yi la'akari da fara kakkaɓo jiragen yaƙi marasa matuƙi na Rasha a sararin samaniyar Ukraine.

    Cibiyar Institute for the Study of War, ce ta bayar da wannan shawara bayan da Rasha ta kai hari a ranar Lahadi kan wata tashar jirgin ƙasa da ke kusa da iyakar Poland.

    Wani jirgin ƙasa da ke ɗauke da manyan jami'an Turai ya wuce wannan yankin jim kaɗan kafin afkuwar lamarin.

    Ukraine ta ce akwai yiwuwar Rasha ta kai harin ne da nufin tarwatsa jirgin.

    A halin yanzu, ƙasashen NATO na kakkaɓo jiragen yaƙi marasa matuƙa na Rasha ne kawai idan sun shiga sararin samaniyar ƙasashen ƙungiyar.

    Sai dai yanzu ana tattauna yiwuwar ɗaukar irin wannan mataki a sararin samaniyar Ukraine, domin kariya da kuma daƙile ƙkaruwar matakan da Rasha ke ɗauka a rikicin da ƙasashen biyu ke yi da juna.

  20. Barka da Safiya!

    Masu bibiyar wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke gabatarwa a kowacce rana, barka da warhaka.

    Da fatan an wayi gari lafiya. Kamar kullum, a yau ma shafin zai ci gaba da kawo muku rahotanni da labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba tare da abokin aiki Usman Minjibir za mu kasance tare da ku zuwa anjima da za mu miƙa ragama ga sauran abokan aiki.

    Sai ku ci gaba da bibiyarmu sannan za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk, X da kuma Instagram domin karanta ƙarin labarai da ma kallon bidiyo.