Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 18/09/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Ana ci gaba da fuskantar ƙarancin wutar lantarki a Gambia

    Ana ci gaba fuskantar rashin wutar lantarki a Gambia, duk da matakin da gwamnati ta ɗauka kan hakan a wasu sassan ƙasar.

    Mazauna wasu yankunan ƙasar sun ce an ɗan samu sauki bayan zanga-zangar da aka yi a makon da ya wuce, da ta kai ga kama sama da mutum 20.

    Kawo yanzu gwamnati ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da an shawo kan matsalar ba.

    Tsohon shugaban hukumar ruwa da lantarkin Gambia, Alpha Robinson, ya shaidawa BBC ɗan saukin da aka samu na da alaƙa da tamakin gaggawa da aka ɗauka na sayen wutar lantarkin daga ƙasashen Senegal da Guinea.

    Shugaban Gambia Adama Barrow ya yi alƙawarin gyara wutar lantarkin kafin karshen watan Oktoba, ta hanyar sayan inji mai karfin 24MW, an kuma bada kwangilar injin solar mai karfin 50MW.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaɓe a watan Disamba mai zuwa, kuma rashin wutar lantarki na daga cikin abubuwan da ma su ƙada ƙuri'a ke kokawa akai.

  2. Yadda farashin man fetur yake a wasu ƙasashen Afirka

  3. Jihar California za ta tsaurara matakai kan AI

    Gwamnan jihar California ta Amurka, Gavin Newsom, ya umarci wani kwamitin ƙwararru da ya gabatar da shawarwari kan yadda za a ƙara tsaurara matakan tsaro wajen amfani da ƙirkirarriyar basirar AI.

    Matakan na iya haɗawa da samar da wani tsari da zai ba da damar dakatar da manhajar AI nan take, idan ta kauce daga abin da aka tsara ta yi aiki a akai ko kuma barazana.

    Wasu daga cikin manyan kamfanonin AI na duniya, ciki har da OpenAI da Anthropic da kuma Nvidia, na da hediƙwatarsu a jihar California.

    Newsom, wanda ɗan jam’iyyar Democrat ne, ya zargi gwamnatin Donald Trump da yin sakaci wajen samar da ƙa’idoji da sa ido kan fasahar AI, yayin da ake ƙara nuna damuwa kan irin barazanar da fasahar za ta iya haifarwa ga bil’adama.

  4. Ana zanga-zangar goyon bayan Saudiyya a Pakistan

    Mai magana da yawun sojin Pakistan Ahmad Sharif Choudry , ya ce kasarsa za ta yi duk mai yiwuwa domin kare martabar ƙasar Saudiyya, a daidai lokacin da tashin hankali ke ƙaruwa tsakanin ƙasar da ƴan tawayen Houthi na Yemen.

    A makon nan ƴan Houthi sun ce Saudiyya ta sake jefa bama-bamai a yankin da suke iko da shi, ya yin da ita kuma ta zargi ƴan tawayen na Yemen da ƙokarin kai harin jirgi maras matuƙa birnin Makka, zargin da suka musanta.

    Chaudhry ya shaidawa kafar yaɗa labarai ta Arab News za su ɗauki duk matakin da ya dace don kare masallatai biyu masu tsarki na Saudiyya da ke Makka da Madina, kuma su na tare da ƙasar ta fuskar soji da diflomasiyya.

  5. Sojojin Kamaru sun ce mayaƙan ISWAP sun kashe fararen hula 14 a ƙasar

    Rundunar sojin Kamaru ta ɗora alhakin wani mummunan hari da ya auku a ƙauyen Madegoua da ke yankin Arewa mai nisa kan ƙungiyar ISWAP ta masu iƙirarin jihadi, tana mai cewa mayaƙan ƙungiyar sun kashe fararen hula 14.

    A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin ƙasar, Kyaftin Cyrille Serge Atonfack, ya fitar ranar Juma'a, ya ce mutum goma da ake zargin mambobin ƙungiyar masu alaƙa da IS ne, waɗanda ke tafiya a kan babura, sun buɗe wa mazauna ƙauyen wuta da gangan a lokacin da suke barci a daren Laraba zuwa Alhamis.

    A cewarsa, "An kashe fararen hula 13 cikin rashin tausayi a wurin harin, yayin da mutum guda ya mutu daga baya sakamakon raunukan da ya samu a asibitin MADA."

    Ya ƙara da cewa an gudanar da jana'izar waɗanda suka mutu bayan harin, yayin da wasu mutum biyu da suka jikkata ke karɓar kulawa ta musamman a asibiti.

    Tun da farko, wani jami'in gwamnati a yankin ya shaida wa BBC cewa maharan sun kuma kwashe kayayyakin mazauna ƙauyen kafin su tsere.

    Rundunar sojin ta ce an ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin yayin da ake ci gaba da sintirin neman maharan.

    A lokaci guda kuma, sojojin sun ce wata fafatawa da suka yi da mayaƙan a kan iyakar Najeriya a ranar Juma'a ta yi sanadin kashe mayaƙan Boko Haram tara tare da ƙwace makamai.

    Fiye da shekara goma yanzu, ƙasashen yankin tafkin Chadi na fama da hare-haren ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi, waɗanda galibi ke haddasa kisa da kuma sace mutane.

    Duk da ƙoƙarin rundunar haɗin gwiwa ta ƙasashe da dama wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya, matsalar tsaro na ci gaba da zama babbar barazana a ƙasashen Kamaru da Chadi da Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar.

  6. Mali da Burkina Faso sun jaddada goyon baya ga Nijar

    Ƙasashen Mali da Burkina Faso sun ƙara jaddada goyon baya ga shugaban mulkin soja na jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani, bayan yunƙurin boren soji a birnin Yamai a watan da ya gabata.

    Manyan wakilan ƙawancen ƙasashen uku na yankin Sahel wato AES, da suka haɗa da ministocin tsaron Mali da Burkina Faso sun gana da Janar Tchiani, domin isar saƙon shugabanninsu da al'umar ƙasashensu.

    Ministan tsaron Burkina Faso Célestin Simpore, ya ce abokan gaba ba sa zaune da siddi, idanunsu kuma na kan ƙasashen, dan haka zama dole su haɗa karfi da ƙarfe domin tsare ƙasashensu.

    A ranar 28-29 ga watan da ya gabata ne sojoji a Nijar suka kai wa sansanonin sojin ƙasar hari, abin da hukumomin ƙasar suka bayyana da yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

    Wannan goyon baya da ƙasashen suka nuna na ƙara fito da haɗin gwiwar ƙasashen da sojoji ke jan ragama, da kuma suka fice daga ƙungiyar ECOWAS.Sai dai masu suka na ganin kai ziyarar bayan makonni 3 da tashin hankalin, ya nuna rashin yin abu a lokacin da ya dace daga ƙawancen na AES duk da tarin ƙalubalen da suke fuskanta na tsaro da tattalin arziki.

  7. Kotun ICC ta yi watsi da ƙarar biyan diyyar aikin wuta na Mambila

    A Najeriya, wata kotun sasanta rikicin kasuwanci ta Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya, wato International Chamber of Commerce tribunal ICC, da ke birnin Paris, ta yi watsi da ƙarar da kamfanin Sunrise Power & Transmission Company Limited ya shigar kan aikin samar da wutar lantarki na Mambilla da ke jihar Taraba.

    Kamfanin dai yana neman a biya shi dala miliyan 680, ciki har da kuɗin yarjejeniyar sulhu da ribar da ta taru, tare da wata ƙara ta daban da ta haura dala biliyan 2.7 a matsayin diyya.

    Rahotanni na cewa kotun ta umarci Kamfanin Sunrise da mai tallafa wa kamfanin, Leno Adesanya, su biya Najeriya kashi 75 cikin 100 na kuɗin shari’ar da ƙasar ta kashe, wanda ya kai kusan dala miliyan 11 da dubu dari 8.

    Rikicin ya samo asali ne daga yarjejeniyar shekarar 2003, wadda ta bai wa Sunrise damar gina aikin samar da wutar lantarki na Mambilla, ta hanyar tsarin gina aikin da gudanar da shi, sannan daga baya a miƙa shi ga gwamnati.

    Kamfanin Sunrise ne ya fara shigar da ƙara a kotun sasanta rikicin kasuwanci ICC a Paris a shekara ta 2017, tare da neman kusan dala biliyan 2.35 a matsayin diyya.

    A shekarar 2020, an cimma yarjejeniyar sulhu, amma rikicin ya sake ɓarkewa bayan gwamnati ta kasa biyan kuɗin da yarjejeniyar ta tanada.

    A 2021 dai binciken BBC ya gano ba a fara aikin wutar Mambila ba, tun da fara maganar aikin a 1982 lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari, amma rahotanni na cewa, a yanzu, gwamnatin Najeriya ta ce tana da niyyar yin aiki da masu zuba jari masu inganci, yayin da take ci gaba da ƙalubalantar zarge-zargen da Sunrise Power & Transmission Company Limited ya gabatar.

  8. An yankewa tsohon ministan Shari'a zaman kaso a Congo

    Kotu a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo ta yankewa tsohon ministan Sahari'ar ƙasar Constant Mutamba ɗaurin shekara 10 a gidan kaso, bayan samun shi da hannu a wata gagarumar danbarwar cin hanci da rashawar kuɗaɗe.

    Mutamba, dai bai halarci zaman kotun daga farko har ƙarshe ba, ya yi watsi da zarge-zargen da hukuncin da ya bayyana da bita da ƙullin siyasa da masu adawa da shi suka kitsa.

    Shari'ar ta maida hankali kan almubazzaranci da kusan dala miliyan 20, da aka ce wai na kuɗin gyaran wata motar alfarma da biyan diyya ga masu ayyukan hukumar FRIVAO ta Uganda a kasar.

    Kotun ta kuma yankewa mataimakin Mutamba, Chancard Bolukola da tsohon shugaban riko na FRIVAO ne daurin shekara 7 da aiki mai tsanani.

  9. Abin da muka sani kan mutuwar masu haar ma'adinai a Neja

    Hukumomi a jihar Neja sun ƙaƙaba dokar hana fita a Minna, babban birnin jihar Neja sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke, bayan mutuwar wasu matasa masu haƙar ma'adai 37 a hannun hukumar tsaro ta Sibil Difens.

  10. Tinubu ya nemi a yi bincike kan mutuwar masu haƙar ma'adinai a Neja

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, waɗanda suka rasu yayin da suke tsare a hannun jami'an Hukumar Sibil Defens a jihar Neja.

    A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, Tinubu ya ce mutuwar mutanen abin damuwa ne matuƙa, yana mai jaddada cewa rayuwar kowane ɗan Najeriya tana da muhimmanci, kuma babu wanda ya kamata ya rasa ransa a yayin da yake tsare a hannun gwamnati sakamakon sakaci, cin zarafi ko gazawar jami'an da ke kula da shi.

    Shugaban ya ce ko da yake gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yaƙi da haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da sauran ayyukan laifi, dole ne jami'an tsaro su gudanar da aikinsu cikin iyakokin doka tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam da martabar duk wanda aka tsare.

    Ya kuma ce idan binciken ya tabbatar da cewa wani jami'i ya taka rawa wajen haddasa mutuwar mutanen ta hanyar sakaci, cin zarafi ko wani mataki da bai dace ba, dole ne a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

    Ya ƙara da cewa dakatar da wasu jami'ai daga aiki ba zai maye gurbin ɗaukar matakin shari'a ba idan hujjoji sun tabbatar da laifi.

    Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan, tare da kira ga al'ummomin da lamarin ya shafa su kwantar da hankalinsu.

    Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta gano gaskiyar abin da ya faru tare da ɗaukar matakin da ya dace, yana mai cewa bai kamata yunƙurin yaƙi da wani nau'in doka ba ya haifar da wani sabon saɓa wa doka ko tauye ƙimar rayuwar ɗan Adam.

  11. A tabbatar da adalci ga masu haƙar ma'adinan da suka mutu a Neja - Atiku

    Jagoran adawar Najeriyar, Atiku Abubakar, ya nemi a tabbatar da adalci kan mutuwar mutanen da ake zargin masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, waɗanda suka rasu yayin da suke tsare a hannun jami'an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Sibil Difens a jihar Neja.

    A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce ya yi matuƙar alhini da kaɗuwa kan mutuwar mutanen, yana mai jaddada cewa duk da zarge-zargen da ake musu, suna da haƙƙin samun kariya da mutuntawa a lokacin da suke tsare a hannun gwamnati.

    Ya ce waɗanda suka mutu mutane ne da ke da iyalai, ciki har da ƴaƴa da iyaye, yan'uwa da masoya, waɗanda suke da haƙƙi daga gwamnati kan kare rayukansu muddin suna ƙarƙashin kulawarta.

    Atiku ya buƙaci a gudanar da binciken cikin ƴanci da adalci da kuma gaskiya, tare da bayyana sakamakonsa ga jama'a.

    Haka kuma ya ce ya kamata a hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin dole, yana mai ƙara da cewa ba ta'aziyya kawai iyalan mamatan ke buƙata daga gwamnati ba.

  12. Labarai da dumi-dumi, Gwamnati ta sa dokar hana fita bayan ɓarkewar zanga-zanga a Neja

    Hukumomi a jihar Neja sun ƙaƙaba dokar hana fita a Minna, babban birnin jihar Neja sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke.

    Wata sanarwa ta hannun sakataren yada labaran gwamnan jihar Ibrahim Bologi ta ce dokar ta fara aiki ne bayan sallar Juma'a, inda za ta rika aiki daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

    Hukumomi sun shawarci jama'a da su mutunta dokar.

    Wani mazaunin Unguwar Tunga Sabon Titi inda zanga-zangar ta fi kamari, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa matasan da suka fusata sun yi ta jefe-jefe yayin da ƴansanda kuma ke harbi.

    A cewarsa, ƴansanda sun harbi mutum huɗu kuma a cikinsu mutum guda ya mutu nan take.

    Da farko, jami'ai sun yi zargin cewa wata cuta ce ta yi sanadin mutuwar matasa da ake zargi da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

    Tuni dai gwamnatin jihar ta Neja ta sanar da kafa kwamitin bincike don gano musabbabin mutuwar matasan

    Lamarin ya sa gwamna Mohammed Umar Bago ayyana makokin kwanaki uku tare da dakatar da yaƙin neman zaɓensa.

  13. Fashewa ta halaka aƙalla mutum 16 a Pakistan

    Wata fashewa da ta afku a wani masallaci da ke arewa maso yammacin Pakistan ta halaka aƙalla mutum 16 tare da raunata fiye da wasu 30.

    Ƴansanda a gundumar Kohat da ke Lardin Khyber Pakhtunkhwa sun ce wata mota maƙare da abubuwan fashewa ta kutsa cikin masallacin yayin da masallata suka taru domin yin sallar Juma'a.

    Jami'an tsaro da dama sun mutu sanadin fashewar.

    Hukumomi sun ce bayan fashewar, an yi musayar wuta tsakanin maharan da jami'an tsaro inda ƴansanda suka kashe ɗaya daga cikinsu.

  14. Ɗalibi ya harbe abokan karatunsa biyu a Philippines

    Wani matashi ɗan shekara 16 ya harbe wasu ɗalibai tare da raunata wasu takwas a wata makarantar sakandare da ke Philippine, daga bisani kuma rahotanni ke cewa ya halaka kan shi.

    Magajin garin yankin ya faɗa wa BBC cewa lamarin ya faru ne a wata makaranta da ke Banga a Lardin Mindanao da ke kudancin ƙasar kuma ɗaliban da suka mutu ƴan shekara 14 ne.

    Albert Palencia ya ce mutane huɗu da suka ji rauni suna cikin mawuyacin hali.

    Cikin wata sanarwa, ma'aikatar ilimi ta ce ta damu matuƙa bisa samun rahoton da ya faru yau Juma'a a makarantar Banga National.

    Wannan ne karo na uku da ake samun irin wannan yanayi na buɗe wa mutane wuta a Philippines tun Yunin bana.

    Palencia ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, lokacin da ɗalibai ke cin abincin rana, sai matashin ya buƙaci abokansa da su je gida saboda bayan cin abincin rana, zai ƙaddamar da wani ƙudiri da yake da shi.

    "Abokansa sun yi dariya saboda maharin mutum ne yawan yin abin ban dariya," in ji Palencia.

    "Bayan an gama cin abincin rana kuma sai ya buɗe wuta. Ya harbi mutum 10 kafin ya halaka kan shi."

    An dakatar da koyarwa sakamakon faruwar lamarin, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

  15. Koriya ta Kudu ta ce ba za ta tura sojoji don taimakawa Amurka a yaƙin Iran ba

    Shugaban Koriya ta Kudu, Lee Jae Myung, ya ce ba zai tura sojoji domin taimaka wa yaƙin da Amurka ke jagoranta a Iran ba, duk da ƙaruwar matsin lamba daga gwamnatin Donald Trump.

    Mr Lee ya ce Koriya ta Kudu ba za ta shiga yaƙin kai tsaye ba, amma yana duba yiwuwar tura wasu kayan aikin soja domin taimakawa wajen kare jiragen kasuwancin ƙasar da ke bi ta Mashigar Hormuz.

    A ƴan makonnin nan, Donald Trump ya buƙaci Seoul ta bayar da gudummawa, yana mai cewa Koriya ta Kudu ta fi dogaro da man da ake samu daga Gabas ta Tsakiya.

    Trump ya kuma rage atisayen soji na haɗin gwiwa da Koriya ta Kudu, sannan ya nuna kusanci ga shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ta hanyar yin kalamai masu kyau game da shi.

    A yau Juma'a, ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu, Cho Hyun, yana Washington domin ganawa da takwaransa na Amurka, Marco Rubio.

  16. Za mu yi duk abin da ya dace don kare Saudiyya – Pakistan

    Wani kakakin rundunar sojin Pakistan ya ce ƙasarsa za ta yi duk abin da ya dace wajen kare Saudiyya.

    Ahmad Sharif Chaudhry ya shaida wa jaridar Arab News cewa Pakistan za ta marawa Saudiyya baya ta fuskar tsaro da diflomasiyya.

    Ya ce “za mu yi abin da ya kamata don tabbatar da tsaron Saudiyya da manyan masallatai biyu mafiya tsarki a duniya.”

    Harin da aka kai kan bututun mai da ke gabas ta yamma da kuma tashar jirgin ruwa ta Yanbu ya janyo dakatar da fitar da mai da Saudiyya ke yi zuwa ƙasashen waje.

    Mayaƙan Houthi sun ce Saudiyya ta sha kai musu hare-hare ta sama .

    Saudiyyan kuma ta zargi Houthi da kai harin da ta bayyana a matsayin na matsorata kan Makkah, zargin da ƴan Houthi suka musanta.

  17. Matasa na zanga-zanga a Neja kan mutuwar masu hakar ma’adanai

    Zanga-zanga ta ɓarke a jihar Neja sakamakon mutuwar wasu matasa masu haƙar ma'adai 37 a hannun hukumar tsaro ta NSCDC.

    Wani mazaunin Unguwar Tunga Sabon Titi inda lamarin ya faru, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa matasan da suka fusata sun yi ta jefe-jefe yayin da ƴansanda kuma ke harbi.

    A cewarsa, ƴansanda sun harbi mutum huɗu kuma a cikinsu mutum guda ya mutu nan take.

    Da farko, jami'ai sun yi zargin cewa wata cuta ce ta yi sanadin mutuwar matasa da ake zargi da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

    Tuni dai gwamnatin jihar ta Neja ta sanar da kafa kwamitin bincike don gano musabbabin mutuwar matasan

    Lamarin ya sa gwamna Mohammed Umar Bago ayyana makokin kwanaki uku tare da dakatar da yaƙin neman zaɓensa.

  18. Nijar ta ƙwace wa mutum biyar takardun zama ƴan ƙasar

    Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya ƙwace wa wasu mutum biyar takardun zama ƴan ƙasar cikinsu har da tsohon Firaiminista Ouhoumoudou Mahamadou kan zarge-zargen yaɗa bayanan da ka iya kawo tashin hankali, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ANP ya bayyana.

    Wata dokar soji da Tchiani ya gabatar ta kuma zargi mutanen biyar, da ke zaune a ƙasashen waje, da haɗa kai da ƙasashen waje da ɓata suna ta intanet da kuma shiga ayyukan da ke neman karya lagon sojoji da kuma raunana tsaron ƙasa da haɗin kan al'umma.

    Hukumomi sun ce an ɗauki matakin ne bisa tanadin dokar da ta samar da rajista ɗauke da sunayen mutane da ƙungiyoyi da kuma cibiyoyi da ake zargin suna da hanu a ayyukan ta'addanci ko kuma ayyukan da ke barazana ga muradun ƙasar.

    Tun bayan samar da rajistar a 2024, hukumomin soji a Nijar sun ƙwace wa sama da mutum 25 takardun zama ƴan ƙasa ciki har da tsaffin ministoci da sojoji da masu fafutuka da kuma masu sukar gwamnatin mulkin soji.

    Matakan wani ɓangare ne na murƙushe ƴan adawa da masu sukar gwamnati tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki a Yulin 2023.

    Mahamadou dai ya riƙe muƙamin Firaminista ne ƙarƙashin mulkin hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

  19. Farashin mai ya sake tashi bayan hare-hare kan bututun man Saudiyya

    Farashin ɗanyen mai ya sake tashi sakamakon rufe wani muhimmin bututun mai a Saudiyya da kuma hare-haren jiragen ruwa a yankin Gulf.

    Farashin ɗanyen mai na Brent ya kai dala 108 kan kowace ganga jim kaɗan bayan da kasuwa ta buɗe.

    Saudiyya ta ce ta rufe bututun man nata da ke gabas maso yammacin ƙasar bayan da wasu jirage marasa matuƙa da aka harba daga yankin Iraq suka lalata shi.

    A baya dai Saudiyya ta zargi ƙungiyoyin mayaƙa da Iran ke marawa baya da kai irin waɗannan hare-hare.

    A gefe guda kuma Oman ta ɗage wani taro da aka shirya yi ranar Litinin tsakanin Iran da ƙasashen Larabawa na yankin Gulf domin tattauna batutuwan da suka shafi Mashigar Hormuz.

  20. An dakatar da shugaban NSCDC a Neja kan mutuwar masu haƙar ma'adanai 37

    Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin dakatar da shugaba hukumar tabbatar da tsaro da kare haƙƙin al'umma, NSCDC a jihar Neja, Suberu Aniviye, sakamakon mutuwar wasu matasa da ake zargin masu haƙar ma'adanai ne ta ɓarauniyar hanya.

    Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayar da umarnin a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X inda kuma ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, da rahotanni ke cewa ya faru a yankin Wushishi/Lukoto da ke Mina, babban birnin jihar ta Neja.

    A cewar sanarwar, an kama waɗanda ake zargi masu haƙar ma'adanai ne ba bisa ƙa'ida ba yayin samamen da aka kai a yankunan jihar a ranar Talata da kuma Laraba na wannan makon.

    A cewar ministan, "muna tafiyar da gwamnati ce wadda babban abin da ta sa a gaba shi ne kare rayukan jama'a kuma muna aiki tuƙuru don tabbatar da hakan".

    Ya kuma buƙaci jama'a da su kwantar da hankalinsu sannan u ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda.

    Tun da farko, gwamnan jihar Neja ta ce an kama kwamandan hukumar.

    Jam'ian hukumar da ke yankin Borgu a jihar sun kama matasan ne bisa zarginsu da hƙar zinare ba bisa ƙa'ida ba.

    Da farko dai, jami'ai sun yi hasashen cewa ɓarkewar cuta ce ta yi sandiyar mutuwar matasan.

    Wakilin BBC ya ce Rahotanni sun nuna cewa matasan sun rasu ne sakamakon cunkoso da rashin isasshen iska a wurin da ake tsare da su.