Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Gasar kofin duniya 2026: Wasan Faransa da Senegal

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
France versus Senegal kick off 20:00
Faransa
20:00
plays
Senegal

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Lokacin da Senegal ta sa Faransa kuka

    Bayan da Brazil, wadda ita ce kasar da ta fi kowacce nasarori a tarihin gasar cin Kofin Duniya, ta kasa doke Morocco, sannan Sifaniya ta tashi kunnen doki da Cape Verde, yanzu kallo ya koma kan yadda za ta kaya tsakanin Faransa da Senegal.

    Wannan shi ne karo na biyu da za su fuskanci juna a gasar cin kofin duniya tun bayan 2002 a Korea/Japan.

    A wasan ne Senegal ta ci 1-0, kuma a lokacin Farance mai rike da kofin nahiyar Turai mai taurari kamar su Patrick Vieira da Thierry Henry da sauransu.

    Shin me zai faru a gasar 2026?

  2. , France v Senegal

    Fitattun yan wasa a filin New York New Jersey

  3. , France v Senegal

    Mun sake dawowa katafaren filin wasa na New Jersey.

    Mai cin yan kallo 78,576 da ake kira filin MetLife, shi ne mafi girma a daukar yan kallo da yawa a gabaki dayan gasar kofin duniya 2026.

    An fara tashi 1-1 tsakanin Brazil da Moroco shi ne zai karbi bakuncin wasan karshe nan da kwana 33 masu zuwa.

  4. Shin me ya faru a wasannin da aka buga a jiya?, France v Senegal

    An fa ci gaba da fafatawa, ga jerin sakamakon wasannin da aka buga a jiya Litinin.

  5. Labarin da ya shafi ƴan wasan da za a fara karawar da su, France v Senegal

    Kylian Mbappe, Michael Olise da Ousmane Dembele da Desire Doue da suka lashe gasar kofin zakarun Turai, suna daga ƴan wasa 11 da Faransa za ta fara karawar da su.

    Sai dai kuwa dan wasan Arsenal, William Saliba wanda ya sha jinya da Rayan Cherki da N'Golo Kante da kuma Bradley Barcola duk suna benci.

    Ƴan wasan Faransa 11: Maignan, Kounde, Saliba, Upamecano, Theo Hernandez, Tchouameni, Rabiot, Olise, Dembele, Doue, Mbappe

    Shi kuwa Idrissa Gueye, wanda bai yi atisaye ba, yanzu ya murmure da shi za a fara wasan.Daga cikin ƴan gaban Senegal sun hada da Nicolas Jackson da mai taka leda a Crystal Palace, Ismaila Sarr da tsohon tauraron Liverpool, Sadio Mane

    Ƴan wasan Senegal 11: Edouard Mendy, Diatta, Koulibaly, Niakhite, El Hadji Malick Diouf, Camada, Idrissa Gueye, Pape Gueye, Ismaila Sarr, Jackson, Mane

  6. , France v Senegal

    Yau fa ana kwana na shida da fara gasar cin kofin duniya 2026 da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.

    Za mu kawo muku wasan da zai yi zafi tsakanin Senegal, wadda ta kai wasan karshe a 2022 da kuma Senegal, wadda karo na uku a jere tana zuwa gasar cin kofin duniya.

  7. An sanar da ƴan wasan da za a fara karawar da su, sannan kuma suna motsa jiki.

  8. Barkan mu da kasancewa a cikin shirin

    Sunana Mohammed Abdu zan kawo muku wasan gasar cin kofin duniya 2026 kai tsaye da za a kara tsakanin Faransa da Senegal a karawar rukuni na tara.

    Za ku iya tafka muhawara a lokacin da muke gabatar da shirin.

  9. Gasar kofin duniya 2026: Me kuke son sani kan karawar Faransa da Senegal?, Gasar kofin duniya 2026

    Tawagar Faransa da ta Senegal za ta kece raini a wasan farko a gasar cin kofin duniya a rukuni na tara ranar Talata.

    Shi ne wasan farko da za a buga a rukunin a Amurka, amma karo na biyu da Faransa da Senegal za su buga gasar kofin duniya, bayan 2002 da Senegal ta ci 1-0 a Korea/Japan.

    Faransa, wadda za ta buga gasar cin kofin duniya karon farko a Amurka na fatan ta kai zagayen karshe karo na uku a jere - bayan lashe kofin 2018 a Rasha da rashin nasara a hannun Argentina a 2022 a Qatar.

    Senegal, wadda take da fitattun ƴan wasa a faɗin duniya, wadda ta lashe kofin Afirka Afcon daga baya aka bai wa Morocco, ta kai zagayen ƴan 16 a Qatar a 2022.

    To sai tawagar Senegal za ta fuskanci kalubale na rashin magoya bayanta da yawa, sakamakon da gwamnatin Amurka ta hana su izinin shiga kasar, kenan sai dai waɗanda ke Amurka su mara mata baya.

    A lokacin da Faransa da Senegal suka kara a 2002, Faransa ce mai rike da kofin da kuma na Fifa Confederation Cup da ta ɗauka a 2001, saboda haka sai aka yi hasshen za a yi tafiyar ruwa da Senegal a karawar.

    To sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙa ba, domin Senegal ce ta yi nasarar cin 1-0 a wasan ta hannun Papa Bouba Diop. Har yanzu ana tuna wasan da kalubalen da Faransa ta fuskanta a fafatawar.

    A wancan lokacin da suka fara haɗuwa, kociyan Senegal na yanzu, Pape Thiaw yana buga wa kasarsa tamaula a shekara 24 baya a lokacin da Senegal ta yi nasarar doke Faransa.

    Saboda haka a yanzu kociyan ya shirya jan ragamar kasar, domin ta taka rawar gani a wasannin bana da za a gwabza tsakanin tawaga48 a karon farko a tarih.

    Wasu ƙididdiga da ya kamata ku sani

    Wasa: Gasar cin kofin duniya 2026 da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico

    Tsakani: Faransa da Senegal

    Ranar wasan: Talata 16 ga watan Yuni 2026

    Filin wasa: New York New Jersyey, Amurka

    Lokacin da za a buga wasan: Karfe 8:00 pm agogon Najeriya da Niger

    Haɗuwa tsakaninsu: Karo na biyu da za su kara a kofin duniya, bayan 2002 da Senegal ta ci 1-0.

    • Duk abin da ya kamata ku sani kan Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026
    • An raba maki tsakanin Brazil da Morocco
    • Gasar kofin duniya 2026: Ghana ta bukaci a duba dalilin hana Partey shiga Kanada

    Me kociyoyin suka ce kafin karawar?

    Didier Deschamps, kocin Faransa:

    "Fara kowacce gasa da kwarin gwiwa abu ne mai kyau da muhimmanci, domin wannan shi ne wasan farko a rukuninmu. Koda yake ba za a ce wannan wasa ne da zai yanke hukunci kan makoma ba, saboda har yanzu akwai sauran wasanni biyu da za a buga daga wannan (a rukuni). Ko a ƙididdiga ma, zakaran kofin duniya na baya da ya wuce ya sha kashi a wasansa na farko. Amma hakan bai hana shi zama zakaran duniya ba daga baya.

    Duk da haka, mafi kyawun yanayi shi ne ka fara da nasara a rukunin da ke a karawar farko mai tawaga huɗu. Wannan ne ko da yaushe burinmu yayin da muke tunkarar wasan farko."

    Pape Thiaw, kocin Senegal:

    "Shin zai zama abin mamaki idan Senegal ta doke Faransa? A gare ni, a'a. Domin muna da ƴan wasa da suke taka leda a manyan mataki a fitattun ƙungiyoyi a duniya. Mun samu tikitin shiga Kofin Duniya sau uku a jere kenan. Haka kuma a gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta baya-bayan nan, mun kai wasan ƙarshe sau uku cikin gasa huɗu.

    Don haka, a gare ni, ba zai zama abin mamaki ba don mun ci Faransa. Na san irin ƙoƙarin da tawagarmu ke yi. Muna ɗaukar wasa ɗaya bayan ɗaya. Za mu kara da kasa mai ƙarfi sosai, musamman idan aka yi la'akari fitattun ƴan wasanta da irin ƙarfin tawagogin da ke a cikin rukuninmu.

    Wannan Kofin Duniya ne, kuma na yi imani cewa kowace kasa ta cancanci kasancewa a nan. A ƙwallon ƙafa, ba na son magana kan yin abin mamaki. Kowacce kasa ta yi aiki tuƙuru domin isa wannan mataki, kuma za mu fuskanci kowanne wasa da burin samun nasara."

    Filin da zai karɓi bakuncin wasan

    Filin wasa na New York New Jersey shi ne zai karbi bakuncin wasan karshe a gasar cin kofin duniya 2026.

    Ya gudanar da babban wasa a ƙwallon zari rugar Amurka wato tsakanin National Football League tsakanin New York Giants da New York Jets, haka kuma ya shirya fafatawa a wasan karshe a 2016 a Copa America Centenario, inda Chile ta doke su Lionel Messi da Argentina a bugun fenariti.

    Fitattun mawaka sun baza basirarsu a filin New York New Jersey daga ciki har da Bruce Springsteen da Beyonce da Ed Sheeran da kuma Taylor Swift.

    A katafaren filin ne aka buga wasan karshe a FIFA Club World Cup 2025, inda Chelsea ta doke Paris St Germain 3-0 ta lashe kofin karkashin koci, Enzo Maresca.

    Shi wannan filin zai karɓi bakuncin wasa biyar a cikin rukuni a gasar cin kofin duniya a bana da guda ɗaya a zagayen kwata fainal.

    Ƴan wasan da ake sa ran fara wasan da su

    Ƴan wasa 11 daga Faransa:

    Maignan; Kounde, Saliba, Upamecano, Hernandez; Tchouameni, Rabiot; Olise; Mbappe, Dembele, Doue

    Ƴan wasa 11 daga Senegal:

    E. Mendy; A. Mendy, Koulibaly, Niakhate, Diouf; Matar Sarr, P. Gueye, L. Camara; I. Sarr, Jackson, Mane