Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Lahadi 4 ga watan Oktoban 2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Mayaƙan TPFL sun fice daga birnin Meƙelle

    Sojojin gwamnatin Habasha tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun ƙwace iko da birnin Meƙelle, wanda shi ne babban birnin yankin Tigray da ke arewacin ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce Mazauna babban birnin yankin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, yayin da sojojin gwamnatin tarayya ke shiga birnin, mayaƙan ƙungiyar TPLF waɗanda suka fara sabon farmaki kwana goma da suka gabata sun fice daga birnin a cikin manyan motocin soja.

    Gwamnatin yankin Tigray Ta ce ta dauki matakin fice wa daga yankin ne na wani dan lokaci da nufin rage tasirin da fadan zai iya yi kan mazauna yankin.

  2. Yemen ta ƙaddamar da hare-haren martani kan mayaƙan Houthi

    Sojojin Yemen sun bayyana cewa suna kai hare-hare kan ƴan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya a babban birnin ƙasar, Sana'a, da kuma yankin Sa'ada da ya kasance babban sansanin ƙungiyar.

    Wani kakakin sojojin ya ce dakarunsu na kai hare-hare ne kan wuraren da ya bayyana a matsayin masu matuƙar muhimmanci.

    Wakilin BBC ya ce, sai dai kuma, da alama Saudiyya ma ta fuskanci hari, inda aka ga hayaƙi da wuta na tashi daga wata cibiyar man fetur ta kamfanin Aramco.

    Tun bayan fara yakin da ake yi da Iran, kungiyar Houthi ta ayyana takunkumin hana zirga-zirgar jiragen ruwa kan Saudiyya, inda take kai hare-hare kan wuraren da ke da muhimmanci da kuma jiragen ruwa, tare da kwace muhimman wurare da ke gabar Bahar Maliya.

  3. Buɗewa

    Masu bibiyar wannan shafi, barkan mu da safiyar Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu cigaba da kawo muku labaran kai-tsaye.

    Ku kasance da mu, inda za mu kawo muku labarai masu ƙayatarwa game da Najeriya da ma ƙasashe maƙwabta, da kuma sauran sassan duniya.