Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Ƙungiyoyi ta Jihar Kano (KSPVIB) ta rufe makarantu masu zaman kansu guda tara na ɗan lokaci saboda rashin cika ka'idojin sake tantance rajista da samun sabbin takardun shaidar aiki.
Sakataren zartarwa na hukumar, Kwamared Baba Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano.
Ya ce makarantu da abin ya shafa za su ci gaba da kasancewa a rufe na tsawon kwanaki bakwai, daga ranar 12 ga Oktoba, 2026, domin ba su bi ƙa'idodin sake tabbatar da rajista da tantancewa da hukumar ta gindaya ba.
Hukumar ta jaddada cewa matakin an ɗauke shi ne domin tabbatar da cewa dukkan makarantu masu zaman kansu a jihar suna aiki bisa ƙa'idoji da dokokin ilimi da aka tanada.
Ana sa ran makarantun za su yi amfani da lokacin rufewar wajen cike dukkan sharuddan da ake buƙata domin a sake ba su damar ci gaba da gudanar da ayyukansu bayan wa'adin kwanaki bakwai ya cika.
Makarantun sun haɗa da; Zayyad Academy, da Success International Schools, da Sunshine International School, da Perfect Schools, da Al-Fa’iq International College, da Mainasara International School, da Shubla Academy, da Darul Mu’uminat Comprehensive School da Hanan International School.
Umar ya ƙarin makarantu 111 da suke tsallake ƙa'idojin yin rijista, da gargadin matuƙar aka tabbatar da hakan za su fuskanci fushin hukuma. A karshe ya yi kakkausan gargaɗi kan makarantu 9 da aka rufe da kar su sake su bude ba tare da izinin hukuma ba in ba haka ba za a ɗauki matakin shari'a akansu.