Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 19/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 19/11/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Imam Saleh

  1. Kotun ICJ ta samu Myanmar da yi wa ƴan Rohingya kinsan ƙare-dangi

    Kotun Ƙasa da Ƙasa ta Duniya ta yanke hukuncin cewa Myanmar ta aikata kisan kare dangi kan tsirarun Musulmin Rohingya, karo na farko da kotun ta samu wata ƙasa da laifin kisan kare dangi.

    Myanmar ta kafa hujjar cewa matakan da ta ɗauka martani ne ga hare-haren da masu tayar da ƙayar baya suka kai, amma kotun ta ce girman hare-haren da yanayin yadda aka aiwatar da su sun wuce kima.

    An kiyasta cewa mutum kusan dubu 10 aka kashe a wani samame da aka kai a arewacin jihar Rakhine a shekarar 2017.

    Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya yi maraba da hukuncin, yana mai cewa dole ne a bai wa 'yan gudun hijirar Rohingya damar komawa gidajensu.

  2. Tinubu zai lashe zaɓen 2027 ba tare da maguɗi ba - Soludo

    Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasar na shekarar 2027 ba tare da maguɗi ba.

    Ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki tana da ƙarfi da kuma tasiri a faɗin ƙasar nan fiye da sauran jam’iyyun hamayya.

    Soludo ya ce ƴan takarar jam’iyyun adawa ba su da irin ƙarfin tasirin da ya kai ko’ina cikin ƙasar, wanda kuma abin da ake buƙata domin ƙalubalantar tikitin APC.

    Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin taron gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban Najeriyar da aka gudanar a dandalin Alex Ekwueme Square da ke Awka, Jihar Anambra.

    Ya ce: “Wannan zaɓe, bisa ga fahimtarmu, tuni an riga an ci shi kuma an sha kaye. Shugaban ƙasa ba ya buƙatar yin maguɗi''

    Soludo ya bayyana cewa Tinubu da mataimakinsa, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, suna da rinjayen siyasa saboda jam’iyyun adawa ba su da ’yan takarar da za su iya samun irin goyon bayan da suke da shi a faɗin ƙasar nan.

  3. Somaliya ta buƙaci jakadan UAE ya fice daga ƙasar

    Somaliya ta umarci jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ya fice daga ƙasar, tana zargin ƙasar da yin katsalandan cikin harkokinta na cikin gida.

    Ministan Yaɗa Labarai na Somaliya bai bayyana takamaiman matakan da suka sa gwamnati ta ɗauki wannan mataki ba, sai dai ya yi gargaɗin cewa gwamnati na ɗaukar matakan kare kanta daga abin da ya bayyana a matsayin wata "bayyananniyar kutse" cikin harkokin ƙasar.

    Matakin ya biyo bayan zargin da Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, ya yi cewa UAE na goyon bayan wasu gwamnatocin yankuna da ke adawa da gwamnatin tarayya da ke birnin Mogadishu.

    A cewar shugaban, irin wannan goyon baya da ake zargin UAE da bayarwa na iya yin tasiri ga zaman lafiyar siyasa da kuma dangantaka tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin yankunan ƙasar.

    Har zuwa yanzu, UAE ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da wannan zargi ko matakin da Somaliya ta ɗauka ba.

  4. Mutum uku sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

    Rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkata biyu a wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a jihar.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Shiisu Adam ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru en a ƙauyen Malamawar Fulani da ke yankin ƙaramar hukumar Garki.

    Ya ce lamarin ya faru ne bayan da aka zargi wasu makiyaya da shigar da dabbobi gonakin manoma domin, abin da ya sa manoman da mutanen ƙauyen suka mayar da martani ta hanyar yunƙurin korarsu.

    ''Sakamakon hakan ne aka samu arangama tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ya haddasa rasuwar mutum uku da raunata biyu,'' in ji shi.

    SP Shiisu ya ce zuwa yanzu hankula sun kwanta a yankin, an ci gaba da gudanar da al'amura.

    ''Kuma muna ci gaba da gudanar da bincike domin kama waɗanda ke da hannu a tashin fitinitar'', in ji kakakin ƴansandan.

  5. An bai wa Putin kujera mai daraja a ganawarsa da Xi da Trump - Rasha

    Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Rasha, TASS, ya ruwaito cewa an bai wa Shugaban Rasha Vladimir Putin kujera mafi daraja a yayin ganawar shugabanni uku da ta haɗa shi da Shugaban China Xi Jinping da kuma Shugaban Amurka Donald Trump.

    A rahoton da kamfanin ya wallafa kan muhimman abubuwan da suka fito daga wannan ganawa ta farko tsakanin shugabannin China, Rasha da Amurka, ya ce Putin ya zauna a hannun daman Xi Jinping, yayin da Trump ya zauna a hannun hagunsa.

    TASS ta bayyana cewa bisa ƙa’idojin diflomasiyya, kujerar da ke hannun daman mai masauƙin baki ita ce mafi girman matsayi ko daraja.

    Har ila yau, kamfanin ya ce Putin ne ya fara magana bayan Xi Jinping ya yi jawabi, sannan Donald Trump ya biyo baya.

    Rahoton ya ƙara da cewa tawagar Putin ta ƙunshi manyan jami’ai da ƙwararru daga muhimman fannoni, ciki har da ministocin kuɗi, harkokin waje da tsaro.

    Haka kuma, tawagogin China da Amurka sun haɗa da manyan jami’ai masu matsayi.

    Ganawar ta ɗauki kusan awa ɗaya da rabi tana gudana.

    TASS ta ce Xi Jinping ya raka Putin har zuwa motarsa, kuma shugabannin uku ba su fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa bayan kammala taron ba.

  6. Netherlands ta yi gargaɗi kan amfani da tabarau mai fasahar AI

    Hukumar kare bayanan sirri ta gwamnatin Netherlands ta shawarci jama'a su guji sayen tabarau masu amfani da fasahar AI, tana mai cewa suna iya zama barazana ga masu amfani da su da kuma mutanen da ke kewaye da su.

    Hukumar ta gudanar da bincike kan nau'o'i shida na irin waɗannan tabarau da ake sayarwa a kasuwar ƙasar, inda ta gano cewa suna iya kawo barazana ga sirrin mutane.

    Haka kuma, ta ce tabarau irin waɗannan na iya zama haɗari domin suna iya bayar da shawarwari marasa inganci ko kuma bayanan da ba su wanzu ba, waɗanda fasahar AI ta ƙirƙira.

    Hukumar ta kuma yi kira ga cibiyoyi da hukumomi su haramta amfani da irin waɗannan tabarau a wuraren da ke buƙatar kariyar bayanai da matuƙar kulawa, kamar asibitoci da kotuna.

    A wani ɓangare kuma, hukumar kare bayanai ta Tarayyar Turai (EU) ta taɓa yin kiran tabbatar da cewa tabarau masu kaifin basira suna nuna a sarari lokacin da suke ɗaukar hoto ko bidiyo, sakamakon damuwa game da yi wa mutane ɗaukar bayanai a ɓoye ba tare da saninsu ba.

  7. KACRAN ta yi wa Tinubu tayin tsarinta na kawar da matsalar tsaro a kwana 45

    Kungiyar Makiyaya Kulen Allah a Najeriya (KACRAN) ta yi wa shugaban Najeriya Bola Tinubu tayin shirinta na kawar da matsalar tsaro cikin kwanaki 45.

    KACRAN ta kuma yaba wa sabon shirin tsaro na shekaru biyar da gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar domin magance matsalar rashin tsaro da ƙasar ke fama da ita.

    A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Hon. Muhammad Khalil Bello ya fitar, ya ce KACRAN ta nazarci shirin, inda ta lura cewa ya ƙunshi matakan ƙarfafa rundunonin tsaro, amfani da fasahar zamani, inganta tattara bayanan sirri, da kuma ɗaukar sabbin jami'an tsaro dubu 78.

    Sai dai KACRAN ta bayyana damuwa kan tsawon lokacin da aka ware domin cimma manufofin shirin.

    A cewarta, al'ummomin da ke fama da hare-hare, garkuwa da mutane da kuma ƙaura daga gidajensu ba za su iya jira har tsawon shekaru biyar ba.

    KACRAN ta yi iƙirarin cewa kashi 80 cikin 100 na matsalar tsaro a Najeriya na da alaƙa da matsalolin zamantakewa kamar rikicin manoma da makiyaya, talauci, rashin aikin yi da jahilci, waɗanda za a iya magance su ta hanyar sulhu da tattaunawa.

    Kungiyar ta ce tana da wani tsarin samar da zaman lafiya cikin kwanaki 45 wanda ya haɗa da sasanci tsakanin manoma da makiyaya da samar da adalci ga waɗanda abin ya shafa, bunƙasa noma da kiwo, samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma ƙarin tallafi ga shirye-shiryen raya yankunan da suka fi fama da matsalar rashin tsaro.

  8. Xi jinping ya yaba da ganawarsa da Putin da Trump

    Shugaban China, Xi Jinping, ya bayyana ganawarsa da Putin da Trump a matsayin mai matuƙar amfani da muhimmanci.

    Shi kuwa Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce ganawar ta buɗe “sabon shafi a tarihin diflomasiyya.”

    Yayin da yake magana da manema labarai bayan ganawar, shugaban na Rasha ya ce taron ya bai wa shugabannin uku damar fahimtar junansu sosai.

    Ya ƙara da cewa ba ya shakku cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya himmatu wajen kawo ƙarshen yaƙin Ukraine da kuma inganta alaƙa tsakanin Washington da Moscow.

    Sai dai Putin ya zargi gwamnatin Kyiv da ƙawayenta na Turai da rashin haƙura da wasu buƙatunsu domin warware rikicin.

    Zuwa yanzu, Shugaba Donald Trump bai ce komai ba game da tattaunawar.

  9. Abin da ya sa dakarunmu suka gana da ƴanbindiga a daji - Sojoji

    Rundunar sojin Najeriya ta yi ƙarin haske kan wani bidiyo da ya nuna wasu jami'anta na ganawa da wasu ƴanbindiga a wani daji.

    A cikin cikin bidiyon wanda ya karaɗa shafukan sada zumunta, an ga jami'an sojoji da na DSS na ganawa da wasu ƴanbindiga riƙe da makamai a tsakiyar wani daji.

    Tun bayan ɓullar bidiyon ake ta aza ayar tambayar abin da ya kai jami'an tsaron cikin daji, ko kuma me suka tattaunawa da ƴanbindigar.

    To amma cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar sun ce jami'an nata sun je dajin ne a wani yunƙuri na sulhu tsakanin ƴanbindigar da jami'an tsaro a jihar Kwara.

    ''Hedikwatar JTF OPSS na son fayyace cewa abin da aka gani a bidiyon wani tsararren matakin tsaro ne da ya shafi sojoji da wasu 'yan bindiga da suka nuna aniyarsu ta miƙa makamansu tare da taimakawa wajen sakin mutanen da suka yi garkuwa da su'', a cewar sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa a yayin ganawar, sojojin sun samu nasarar karɓar bindigogi kirar AK-47 guda 12, sannan kuma ƴanbindigar suka saki wasu mutum 10 da suka yi garkuwa da su.

  10. Isra'ila ta ce ta kawo ƙarshen farmakin da ta ƙaddamar a Gaza

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kawo ƙarshen farmakin da suka ƙaddamar a Gaza tun ranar Laraba.

    A cikin wata sanarwa, hukumar ma'aikatar tsaron Isra'ila da ke kula da harkokin fararen hula a yankunan Falasɗinu ta ce an sake bai wa Falasɗinawa damar zirga-zirga a yankunan da abin ya shafa da ke kusa da sansanonin ƴan gudun hijira na Bureji da Nuseirat, bayan layin rawaya.

    Layin rawayar dai shi ne iyakar da sojojin Isra'ila suka ayyana domin raba yankunan da suke iko da su da sauran sassan Gaza.

    Tun da farko dai sojojin Isra'ila sun umarci mazauna yankin su fice daga wuraren kafin fara aikin soja.

  11. 'Putin ya ji daɗin ganawa da Trump'

    Mai bai wa shugaban Rasha shawara kan harkokin Waje, Yuri Ushakov, ya ce Shugaba Vladimir Putin na cikin farin ciki sosai bayan ganawarsa da Shugaba Trump na Amurka.

    Da yake zantawa da gidan talabijin na gwamnatin Rasha, Vesti, Ushakov ya ce tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta gudana cikin nasara.

    Kafofin yaɗa labaran Rasha sun yaɗa wani bidiyo da ke nuna Trump na shiga ɗakin taro yana tunkarar Putin tare da cewa: Wannan abokina ne!"

    A cewar Ushakov, yaƙin Ukraine ne ya kasance babban abin da aka fi mayar da hankali a kai a ganawar, wadda ta ɗauki tsakanin minti 35 zuwa 40.

    Ya ce shugabannin sun kuma tattauna kan alaƙar ƙasashen Amurka da Rasha.

    Fadar Kremlin ta ce babu wani daga cikin shugabannin da ya yi wata muhimiyar sanarwa bayan ganawar, yayin da ɓangarorin biyu ke shirin wata ganawa da Shugaban China Xi Jinping daga baya a yau.

  12. Kwale-kwale ya kife a Senegal ɗauke da sama da mutum 100

    Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto da neman waɗanda suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da baƙin haure ya kife a gaɓar tekun Senegal.

    Wani da ya tsira daga haɗarin ya shaida wa ƴan sanda cewa akwai kusan mutum 100 a cikin kwale-kwalen.

    Jami'an yankin sun ce ƙaramin jirgin ya bugi wasu duwatsu kafin ya nutse a ranar Laraba.

    Lamarin ya faru ne ƙasa da mako guda bayan da baƙin haure 43 suka mutu sakamakon hatsarin wani jirgin ruwa a gaɓar garin Thieppe da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    A shekarun baya-bayan nan dai dubban ƴan yammacin Afirka sun rasa rayukansu yayin da suke ƙoƙarin tsallaka Tekun Atlantika zuwa Tsibiran Canary na ƙasar Spain, cikin neman ingantacciyar rayuwa.

  13. Musulunci zai fi kowane addini yawan mabiya nan da 2035 - Bincike

    Wata cibiyar bincike ta Amurka ta yi hasashen cewa addinin Musulunci zai zama addini mafi yawan mabiya a duniya nan da shekarar 2035, inda zai zarce Kiristanci.

    Binciken da cibiyar Pew Research Center ta gudanar ya nuna cewa yawan mabiya addinin Kirista na ci gaba da ƙaruwa, amma yawan Musulmai na ƙaruwa cikin sauri saboda yawan haihuwa da ya fi yawa a tsakanin Musulmai.

    Rahoton ya ce ana ƙiyasin cewa mace Musulma na haihuwar yara fiye da uku a matsakaici, idan aka kwatanta da kusan yara biyu da rabi ga mace Kirista.

    Tun shekaru shida da suka gabata, Musulmai suka kasance masu rinjaye a ƙasashe 53 na duniya.

    Ana sa ran mafi yawan ƙaruwar yawan Musulman za ta faru ne a waɗannan ƙasashe.

    Binciken ya kuma hasashen cewar adadin Musulmai zai ƙaru da ƙarin mutum biliyan 1.2 nan da shekarar 2070.

  14. An ci gaba da musayar wuta tsakanin Saudiyya da Houthi

    An sake samun musayar wuta a tsakanin Saudiyya da kuma 'yan tawayen Houthi a Yemen.

    Mahukuntan Saudiyya sun ce sun daƙile wani harin makami mai linzami da aka kai kan birnin Riyadh, sai dai rahotanni sun nuna tarkacen makamin da ya faɗo ya haddasa ɓarna a wasu wurare.

    A nasu ɓangaren, ƙungiyar Houthi ta ce jiragen yaƙin Saudiyya sun kai hare-haren sama kan babban birnin Yemen, Sanaa.

    Tun da farko Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya gana da babban kwamandan rundunar sojin Amurka a yankin, Admiral Brad Cooper, inda suka tattauna kan halin da ake ciki.

    Faɗan da ake tsakanin ƙawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta da kuma mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran ya ƙara tsananta a watan jiya.

  15. Trump ya fara ganawa da Putin a China

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya fara tattaunawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin a ƙasar China, gabanin wata ganawa ta musamman da za su yi tare da Shugaban China Xi Jinping.

    Ana sa ran shugabannin ƙasashen uku za su haɗu a wani taron ƙoli na tarihi da ba a taɓa yin irinsa ba.

    A farkon ganawarsa da Mista Putin, Shugaba Trump ya ce suna da kyakkyawar alaƙa, yana mai cewa taron na iya haifar da "abubuwa masu kyau da dama" ga ɓangarorin da abin ya shafa.

    Shugabannin uku suna da bambancin ra'ayi a kan abin da suke son a cimma a yayin wannan taro, inda shugaba Trump ke son a samu ci gaba amma ta fannin abin da zai daɗaɗawa Amurkawa.

    Ƙasar China ta ce shugabannin za su yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya a duniya.

  16. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta da zaurenmu na Whatsapp domin samun arin labarai da bidiyoyi.