Nan muka kawo karshen shirin
Da fatan za ku ci gaba da bibiyar BBC Hausa, don kawo muku sharhi da bayanan wasannin cin kofin duniya da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Sunana Mohammed Abdu nake yi muku fatan alheri. Sai da safe.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammed Abdu tare da taimakon AI
Da fatan za ku ci gaba da bibiyar BBC Hausa, don kawo muku sharhi da bayanan wasannin cin kofin duniya da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Sunana Mohammed Abdu nake yi muku fatan alheri. Sai da safe.
Ingila ta samu maki uku a kan Croatia, bayan nasara da cin 4-2 a wasan farko a rukuni na 12.
Sai da tsakar dare Ghana za ta kece raini da Panama.
An buga kwallo ta fada cikin yan kallo, wani ya kama ya rike ba zai bayar ba, zai ajiye a matsayin tarihi da zai nunawa yan baya.
Kowa ya samu dama mai kyau tsakanin Croatia da Ingila, amma babu wadda ta amfana.
Muna daf da tashi daga karawar nan, kuma wasan ya yi kyau an ci kwallo shida.
Na manta ban sanar da ku cewar dan wasan Manchester City, Marc Guehi ya canji takwaransa, John Stones.
Ko Ingila za ta hada maki uku a wasan farko a rukuni na 12 ko kuma Croatia za ta yi wani abin kafin lokaci ya cika?
Saka ne ya jawo kwallon daga gefen dama ya kuma bai wa Rashford daga gefen hagu, shi kuma ya shiga gidan Croatia, sai da ya dakatar da dan wasa sannan ya buga ta fada raga.
Rashford ya koma kan ganiya tun bayan da ya buga wasannin aro a kakar da ta wuce a Barcelona daga Manchester United.
Kadan ya rage sabon dan wasan Ingila da ya shiga wasan ya ci kwallo, wato Spence ya buga kwallon amma ta taba mai tsaron ragar Croatia.
Rashford yana jan kwallo daga bangaren hagu, har yanzu bai samu wata babbar dama ba.
Martin Baturina ya fita daga filin, inda Nikola Vlasic ya maye gurbinsa.
A Ingila kuwa, Jude Bellingham ya fita, yayin da Djed Spence ya samu damar shiga filin.
Croatia ta nemi ragar Ingila, amma mai tsaron ragar Ingila, ya kama kwalon cikin ruwan sanyi.
Wadanda suka shiga wasan sun hada da Morgan Rogers da Marcus Rashford da kuma Bukayo Saka.
Wadanda aka cire sun hada da Declan Rice da Anthony Gordon da kuma Noni Madueke.
An shiga gangare a wasan, kenan kasa da minti 20 za a tashi daga karawar, kuma wannan sakamakon ya yi wa Ingila daidai idan har za a tasghi haka.
Ta saka Marco Pasalic da Igor Matanovic, sun maye gurbin Luka Vuskovic da kuma Petar Musa.
Yadda Ingila ta mamaye karawar nan
Kyaftin, Luka Modric ya fita daga wasan, yayin da Mateo Kovacic ya maye gurbinsa.
Golan Croatia, Livokovic ya cancanci jinjina, yadda yake haka Ingila zura masa kwallo a raga, Ingila ta matsa sai ta kara, ganin ita take cin kwallo ana farkewa.
Ta kwan da sanin cewa maki uku a wasan farko a cikin rukuni yana da mahimmaci.