Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Gasar kofin duniya 2026: Ingila ta fitar da DR Congo a zagayen ƴan 32

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagayen ƙasashe 32
England 2 , Congo DR 1 at Full time
Ingila
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
Full time
Hutun rabin lokaci Ingila 0 , Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo 1

Key Events

Ingila

  • H. KaneGoal 75 minutes, Goal 86 minutes

Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

  • B. CipengaGoal 7 minutes
Ba da ƙwallo a ci
Ingila,A. Gordon (75 minutes, 86 minutes)
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo,C. Mbemba (7 minutes)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da taimakon AI

  1. An tashi wasan, Ingila 2-1 DR Congo

    Ingila ta kai zagayen yan 16, bayan doke DR Congo 2-1 a wasan yan 32 a gasar cin kofin duniya.

    DR Congo ce ta fara cin kwallo tun a minti na bakwai da fara wasa daga baya Ingila ta farke a zagaye na biyu ta kuma kara na uku.

  2. An yi karin minti shida, Ingila 2-1 DR Congo

  3. Ingila ta yi canjin dan wasa, Ingila 2-1 DR Congo

    Declan Rice ya nuna alama yana fama da ciwo, nan da nan Tuchel ya saka John Stones ya maye gurbinsa..

  4. , Ingila 2-1 DR Congo

    Wannan shi ne kwallo na 13 da Harry Kane ya ci a gasar cin kofin duniya jimilla. Kuma na biyar a wannan gasar cin kofin duniya ta 2026, saura ɗaya ya kamo Messi da Mbappe masu shida-shida a raga..

  5. GOAL - England 2-1 DR Congo, Harry Kane

    Kyaftin din tawagar Ingila ya ci kwallo mai kyau a tsakanin masu tsaron bayan DR Congo kuma daf da gida haka ya karbi kwallo ya kuma buga ko kallon raga bai yi ba, amma hakan ya ci kwallon ta fada ragar DR Congo - wadda take neman ganin samu ta rasa.

  6. , Harry Kane (75 mins)

    Inda Ingila ta farke sai kai kora take gidan DR Congo, amma ta kasa samun damar kara kwallo na biyu.

    Wissa yana daga can sama, yana fatan ya samu kwallo ya tsinke zuwa gidan Ingila.

  7. GOAL - England 1-1 DR Congo, Harry Kane

    Harry Kane ya farkewa Ingila kwallon da kai, kuma ta huɗu a gasar nan kuma ta hudu a zagayen ziri daya kwale.

    Wasan ya koma sabo.

  8. , Ingila 0-1 DR Congo

    Ana ci gaba da wasan, amma har yanzu Ingila ba ta samu wata gagarumar dama ba tun bayan da suka sha ruwa aka ci gaba da wasan.

  9. An koma wasan bayan shan ruwa, Ingila 0-1 DR Congo

    Ingila ta yi canji, inda ta cire mai tsaron baya, Djed Spence ta maye gurbinsa da dan gaba, Eberechi Eze.

    Kenan Ingila za ta ci gaba da kai hari kenan.

  10. An busa hutun shan ruwa, England 0-1 DR Congo

    DR Congo ta tsare bayanta da kyau sosai, har yanzu Ingila na neman farke kwallo kafin ta sa me za ta yi nan gaba.

  11. DR Congo ta sauya dan wasa, Ingila 0-1 DR Congo

    Nathanael Mbuku ya fita daga wasan an kuma sac Meschack Elia madadinsa a DR Congo.

  12. Ingila ta yi sauyin yan wasa biyu, Ingila 0-1 DR Congo

    Ingila ta fitar da Noni Madueke da Marcus Rahford ta kuma maye gurbinsu da Anthony Gordon da kuma Bukayo Saka.

  13. , Ingila 0-1 DR Congo

    Kowanne lokaci za a iya fara canjin yan wasa kowacce tawaga tana da damar yin canji biyar-biyar, amma da yake wasa da saura sai an yi taka tsantsa, wata kila a tashi a minti 90 ko kuma ya kai 120.

  14. , Ingila 0-1 DR Congo

    Ingila na rike kwallo tana rabawa hagu da dama da tsakiya, Rashfod ya buga cikin gidan DR Congo, amma ta yi yawa ta yi waje.

  15. , Ingila 0-1 DR Congo

    Rashford ya kara samun dama ya buga da karfi amma golan DR Congo ya taba ya kuma fadi kasa kwallon na sama, mai tsaron bayan DR Congo ya buga, babu wani hadari a wannan lokacin.

  16. , Ingila 0-1 DR Congo

    Rashford ya samu daama daga gefen hagu a gidan DR Congo kuma irin yadda aka ci Ingila, sai dai ya buga kwallon ta yi waje.

  17. An koma zagaye na biyu, Ingila 0-1 DR Congo

    Za su kara buga minti 45, za kuma su je hutun shan ruwa, idan Ingila ta farko aka kai minti 90 ana 1-1 sai karin lokaci da kuma bugun fenariti.

    Idan kuma haka aka tashi DR Congo ta kai zagayen yan 16 a karon farko a gasar kofin duniya karo na biyu da take halarta.

  18. Yadda aka buga zangon farko, England 0-1 DR Congo

  19. , England 0-1 DR Congo

    Ingila ba ta taba cin wasa ba a gasar cin kofin duniya da zarar an fara zura mata kwallo daga tara baya, inda aka doke ta bakwai daga ciki da canjaras biyu.

  20. An je hutun rabin lokaci, Englnd 0-1 DR Congo

    Za su huta minti 15 daga nan su dawo a karasa zango na biyu da za a yi minti 45.