Iran ta yi watsi da tayin Oman na karɓe iko da mashigar Hormuz
Iran ta yi watsi da tayin Oman na karɓe ikon gudanar da mashigar ruwan Hormuz ta hanyar haɗin gwiwa da Iran.
Wani babban jami’in ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba cewa hakan ba za ta saɓu ba.
Hakan ya dusashe fatan samun mafita ga taƙaddamar da ta janyo dakatar da harkokin kasuwanci a yankin Tekun Fasha na tsawon watanni.
Oman ta gabatar da wata sabuwar yarjejeniya ga ƙasashen yankin domin warware rikicin da ya shafi wannan muhimmiyar mashigar ruwa.
Sai dai Tehran ta ƙi amincewa da shirin Oman na gudanar da mashigar Hormuz tare da sauran ƙasashen yankin, tana mai cewa shirin ba shi da wata damar nasara.
Jami’in ya shaida wa Reuters cewa Amurka da Saudiyya na ƙoƙarin matsa wa Oman lamba domin aiwatar da abin da ya kira “tsare-tsare marasa tushe na zahiri” game da wannan muhimmiyar mashigar ruwa.
Ya ƙara da cewa Iran na nan daram kan matsayinta na cewa duk hanyoyin zirga-zirgar ruwa da ke cikin mashigar Hormuz, da kuma wani ɓangare na hanyoyin da ke fita daga gare ta, ya kamata su kasance ƙarƙashin ikon Iran.