Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 16/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 16/07/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Rundunar Sojin Najeriya ta cafke baƙin haure 24 a Legas

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wasu baƙin haure 24 da ba su da takardun zama a ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulɗa da jama'a na rundunar ta 81, Laftanar Kanal Musa Yahaya ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an kama mutanen ne a yayin wani a wani samame da ta kai a ƙaramar hukumar Epe da ke jihar Legas.

    Ta ce ta kai samamen bayan bayanan sirri da suka nuna akwai wasu baƙin haure da ba su da takardun izini a yankin.

    Sanarwar ta ce sojoji tare da haɗin gwiwar jami'an sa-kai ne suka kai samame wani gida a yankin Imokun da ke Odo-Noforija/Poka, inda suka kama mutum 24 - maza 15 da mata 9.

    Binciken ya nuna cewa mutum 10 daga cikin waɗanda aka kama ƴan Kamaru ne, 6 daga Togo, uku-uku daga Côte d’Ivoire da Jamhuriyar Benin, sai ɗaya-ɗaya daga Burkina Faso da Guinea-Bissau.

    Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin tantance matsayin shigowarsu Najeriya, dalilin zamansu da kuma ko suna da hannu a wasu ayyukan da suka saɓa wa doka.

    Haka kuma, jami'ai na ƙoƙarin gano mai gidan da aka kama su a ciki domin yi masa tambayoyi kan yadda suka zauna a wurin da kuma irin ayyukan da suke gudanarwa.

    Daga bisani an miƙa mutanen ga hukumar kula da shige da fice ta Najeriya reshen jihar Legas domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan da suka dace.

  2. An jiyo ƙarar fashe-fashe a birnin Dubai

    Rahotanni na cewa an ji ƙarar wasu fashe-fashe a tsakiyar birnin Dubai da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ranar yau Alhamis.

    Wasu majiyoyi sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ba san takamaimai inda aka samu fashwar ba.

    Sai dai har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan musabbabin fashe-fashen ba, kuma hukumomi ba su bayyana ko an samu asarar rayuka ko jikkata ba.

    Sai dai hukumomin Dubai sun musanta rahotannin da suka ce an ji ƙarar fashe-fashe a tsakiyar birnin.

    Ofishin Yaɗa Labarai na Dubai ya fitar da sanarwa yana mai cewa ba a samu wata fashewa a tsakiyar birnin ba.

    Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ke ci gaba da ƙamari, bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin samar da wutar lantarki na Iran, yayin da Tehran ke zargin Washington da karya yarjejeniyar da ke tsakaninsu tare da yin barazanar mayar da martani idan aka kai mata wani sabon hari.

  3. Iran ta zargi Amurka da aikata laifukan yaƙi

    Iran ta zargi Amurka da aikata laifukan yaƙi, tana mai cewa matakin da Amurka ta ɗauka na sake kakaba takunkumin kan Iran ya saɓa wa yajrjeneiyar da ƙasashen biyu suka cimma.

    A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar, ta ce Amurka ta kai hare-hare kan wasu cibiyoyin fararen hula da na gwamnati a Iran da suka haɗa da cibiyar jinya ta runduna ta 388 a Bampour da ke Iranshahr, rumbun ajiyar alkama na Hoveizeh da kuma hasumiyar sa ido ta sojojin ruwa a Chabahar.

    Iran ta bayyana waɗannan hare-hare a matsayin "laifukan yaƙi."

    Ma'aikatar ta kuma yi zargin cewa wannan ne karo na uku cikin shekara guda da Amurka ke kai wa Iran hari a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

    A sanarwar, Tehran ta buƙaci ƙasashen yankin da kada su bari a yi amfani da ƙasashensu ko sararin samaniyarsu ko ruwansu wajen kai wa Iran hari.

    Iran ta ce tana son ci gaba da haɗa kai da ƙasashen yankin ba tare da sa hannu ko katsalandan daga Amurka ba.

    Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar dokokin Iran, Mohammad Saleh Jokar, ya gargadi ƙasashen yankin Tekun Fasha da su guji bai wa dakarun Amurka damar amfani da yankunansu da gabar tekunsu.

  4. Hezbollah ta musanta zargin safarar makamai zuwa Lebanon, Syria ta ce ta kama wasu makamai da ta yi zargin an yi niyyar aika wa Hezbollah

    Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta musanta zargin da hukumomin Siriya suka yi cewa tana safarar makamai da makamai masu linzami daga Siriya zuwa Lebanon.

    A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na ƙungiyar ya fitar, Hezbollah ta bayyana zarge-zargen a matsayin "ƙage marasa tushe."

    Ƙungiyar ta ce manufar yaɗa irin waɗannan zarge-zarge ita ce bata mata suna da kuma yi wa abin da ta kira "shirin Amurka da yahudawan a yankin".

    Hukumomin Syria dai sun ce sun daƙile wani yunkurin shigar da wasu makamai da makamai masu linzami ta iyakar ƙasar da Iraki.

    Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Syria SANA ya ambato wata majiya daga ma'aikatar harkokin cikin gidan ƙasar na cewa bincike ya nuna an yi niyyar kai makaman ne ga ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon.

    Shugaban Amurka Donald Trump dai ya bayyana a watan Yuni cewa ya tattauna da shugaban Syria Ahmed al-Sharaa kan hanyoyin da za a bi wajen daƙile ayyukan Hezbollah.

  5. Kotu ta soke hukuncin da ya haramta wa INEC tsara jadawalin zaɓen 2027

    Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin wata babbar kotun tarayya da ta ce hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC, ba ta da ikon tsara jadawalin gudanar da zaɓen fidda gwani da kuma tsayar da ƴan takara gabanin babban zaɓen 2027.

    A hukuncin da alkalan kotun suka yanke baki a ranar Alhamis, kotun ta tabbatar da cewa jadawalin da INEC ta fitar na shirye-shiryen zaɓen 2027 yana nan daram.

    Yayin karanto hukuncin, Mai Shari'a Okon Abang, ya ce jam'iyyar Youth Party (YP), wadda ta shigar da ƙarar, ba ta da hurumin kalubalantar jadawalin INEC.

    Kotun ta ce jam'iyyar ta kasa bayyana yadda jadawalin da INEC ta fitar ya tauye mata haƙƙinta ko ya hana ta gudanar da zaɓen fidda gwani domin shiga zaɓen 2027.

    Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin cewa INEC tana da iko a doka ta fitar da jadawalin zaɓen, tare da cewa babbar kotun tarayya ta yi kuskure lokacin da ta amince da buƙatun da jam'iyyar ta gabatar.

    Kotun ta kuma ce jam'iyyar siyasa za ta iya zuwa kotu ne kawai idan an take haƙƙinta na shiga zaɓen 2027.

    A watan Mayu ne, Babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa INEC ba ta da ikon sanya wa jam'iyyun siyasa lokacin da za su gudanar da zaɓen fidda gwani ko tsayar da ƴan takara.

  6. An dakatar da loda mai a tashar ruwan Iraki bayan wani hari ya faɗa kan tankar mai

    An dakatar da loda ɗanyen mai a tasoshin mai na Iraƙi bayan wani jirgi maras matuƙi ya bugi tankar mai

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito daga wasu majiyoyi tsaro da man fetur huɗu cewa an dakatar da loda ɗanyen mai a dukkan tashoshin man fetur na ƙasar a ranar Alhamis bayan wani harin jirgi maras matuƙi kan wata tankar mai a tashar man fetur ta Basra.

    Rahoton ya ce harin da jirgin maras matuƙin ya kai bai haddasa wata ɓarna ko tashin gobara ba.

    Tasoshin man fetur na Iraƙi suna kudancin ƙasar, kuma har yanzu ba a tabbatar da inda aka harbo jirgin marar matuƙin ba.

    Reuters ya ce hukumomin Iraƙi sun fitar da tankar man daga tashar ruwan tare da wata tankar mai ta daban a matsayin kariya.

    Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Iraƙi ya kuma ruwaito, ba tare da yin ƙarin bayani ba, cewa wani jirgi maras matuƙi ya faɗi a tashar ruwa ta Faw da ke Iraƙi a ranar Laraba, amma bai haddasa wata ɓarna ba.

  7. MDD ta nuna damuwa kan rahotonnin mutuwar ƴan Rohingya 500

    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matuƙar damuwa game da rahotannin da ke cewa wasu jiragen ruwa biyu ɗauke da sama da mutum 500 ƴan ƙabilar Rohingya masu neman mafaka sun kife a kusa da gaɓar tekun ƙasar Myanmar.

    Jiragen ruwan sun tashi daga yammacin Myammar mako biyu da rabi da suka gabata, kuma tunda daga wannan lokacin ba a sake jin labarin mutanen 530 da ke cikin jiragen ba.

    Sama da 'yan ƙabilar Rohingya miliyan ɗaya ne ke zaune a sansanonin ƴan gudun hijira a ƙasar Bangladesh, bayan da sojojin Myanmar suka kora su daga ƙasar shekaru tara da suka gabata.

    Tsirarun musulman ƴan Rohingya sun samu kansu a tsakiyar yaƙin basasar Myanmar a birnin Rakhine, suna fuskantar wariya da tashin hankali da kai musu hare-hare, lamarin da ya tilasta wa wasu daga ciki tafiyar Hadari da tsallaka tekun Andaman domin tsallakawa kasar Malaysia.

    Kusan babu wata kafar da ake iya jin halin da ake ciki a jihar Rakhine, amma ƙungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce an gano gawarwakin mutane da ruwa ya turo su a wurare biyu, da ake kyautata zaton na waɗanda ke cikin kwale-kwalen da ya nutse ne.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana bukatar samar da hanya ingantacciya domin ‘yan Rohinja da ke neman mafakar siyasa, sakamakon yadda ɗaruruwa ke mutuwa a teku, wasu kuma masu safarar mutane na cin zarafinsu.

    Sai dai babu wata kasa da ta nuna aniyar taimaka msu, ko saukaka hanyoyin da suke balaguron.

  8. Gobara ta kashe mutum 11 a cibiyar kula da yara ta Aljeriya

    Mutum 11 ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wata cibiyar kula da yara da ke Algiers, babban birnin ƙasar Aljeriya.

    Hukumar kare fararen ta ƙasar ta ce gobarar, wadda ta tashi da tsakar dare, ta kuma raunata mutum 19.

    Jami'an hukumar sun ce har yanzu suna aiki domin kammala daƙile wutar.

    Zuwa yanzu hukumar ba ta bayyana maƙasudin tashin gobarar ba.

    Aljeriya ta kwashe kwanaki tana fama da tsanann zafin rana, yayin da kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton samun gobara fiye da 1,000 a ƙasar cikin mako guda.

    Hukumar kare muhalli ta ƙasar ta ce an samu rahotonnin gobarar daji 115 a cikin kwana guda.

    Shugaban ƙasar, Abdelmadjid Tebboune ya aike da saƙon jaje ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa a cibiyar kula da ƙananan yaran, bayan mai bayyana lamarin da ''babban rashi''.

  9. Wasu daga cikin kadarorin Abubakar Malami da EFCC ta ƙwace

    A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umanin ƙwace wasu kadarorin tsohon ministan sharia'ar Najeriya, Abubakar Malami

    Kotun ta ce ta bayar da umarnin ne saboda ta gano cewa ya mallaki kadarorin ne ba bisa ƙa'ida ba.

    EFCC ce dai ta shigar da ƙara ta buƙatar ƙwace kadarorin tsohon ministan guda 57 na dindindin da darajarsu ta kai naira biliyan 212.8.

    Abubakar Malami ya kasance ministan shari'ar Najeriya zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023.

  10. Jerin kadarori 48 da EFCC ta ƙwace daga Abubakar Malami

    A ranar Larabar nan ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙwace kadarori masu alaƙa da tsohon ministan shari'ar zamani marigayi Muhammadu Buhari, Abubakar Malami, domin miƙa su ga gwamnatin tarayya.

    Da take yanke hukuncin, mai shari'a Joyce Abdulmalik ta ce hukumar EFCC ta riga ta tabbatar da cewa kadarorin da aka ƙwace an same su ne ba ta halastacciyar hanya ba.

    Kotun ta ara da cewa Malami ya gaza gamsar da ita cewa ya mallaki kadarorin nasa ne ta hanyar halaliya.

    Domin ganin kadarorin da aka ƙwacen karanta cikakken labarin a nan

  11. Iran ta ce ta kakkaɓo jirgin Amurka maras matuƙi

    Iran ta ce ta kakkaɓo jirgin Amurka maras matuƙi samfurin MQ-9, wanda ta ce yana shawagi a saman birnin Andimeshk.

    A cewar dakarun juyin juya halin ƙasar, an kakkaɓo da jirgin ta hanyar amfani da sabbin makamanta na tsaron sararin samaniya.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim mai alaƙa da rundunar juyin juya halin ƙasar, ya ce aikin kakkaɓo da jirgin ya yi nasara, amma bai bayar da shaidar da za ta tabbatar da iƙirarin ba.

    Kawo yanzu gwamnatin Amurka da rundunar sojin ƙasar ta CENTCOM, ba su tabbatar da iƙirarin ba.

  12. Amurka da amince da sayar wa Saudiyya da Kuwait makamai

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da sayar wa Saudiyya makamai na kusan dala biliyan 1.96 domin ƙarfafa tsarin kariyar sararin samaniyar ƙasar.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da rikice-rikice ke ƙara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

    "Sayar da ya samu goyon bayan manufofin harkokin wajen Amurka da kuma muradun tsaronta ta hanyar ƙarfafa tsaron wata muhimmiyar ƙawa da ba mambar ƙungiyar NATO ba''.

    ''Saudiyya na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki a yankin Tekun Fasha." a cewar sanarwar ma'aikatar wajen Amurkan.

    Ma'aikatar ta kuma bayyana cewa yarjejeniyar sayar da makaman ta ƙunshi na'urorin sarrafa makamai masu linzami har 20,000, waɗanda za a yi amfani da su wajen hare-hare ta sama da ta ƙasa.

    Yarjejeniyar ta kuma haɗa da na'urorin harba makamai da bama-bamai da kayayyakin gyara da horaswa da kuma tallafin dabaru da sufuri.

    Haka kuma ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ta amince da wani ƙunshin tallafi daban na dala miliyan 484 ga Kuwait domin tallafin fasaha ga jiragen sama.

    Ana sa ran kammala da aiwatar da waɗannan yarjejeniyoyin bayan majalisar dokokin Amurka ta yi nazari tare da amincewa da su.

  13. Mun kai hari kan sadarwar Amurka da tankokin mai a Jordan - Iran

    Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ambato rundunar sojin ƙasar na cewa sun kai hari kan cibiyar sadarwar Amurka da wasu tankokin mai na sojojin Amurka a Jordan.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ce ''Iran ta yi amfani da jirage marasa matuƙa na yaƙi wajen ƙaddamar da hare-haren cikin dare a sansanin sojin Amurka na Al-Azraq da ke Jordan''.

    ''A wannan sansanin ne aka girke na'urorin kakkaɓo makaman linzami, kuma ana kallaonsa a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyi mafiya muhimmanci ga Amurka da yankin Yammacin Asiya'', kamar yadda Tasnim ya rubuta.

  14. Pakistan ta yi kira ga Iran da Amurka su koma teburin sulhu

    Ƙasar Pakistan ta ce ta yi kira ga Amurka da Iran su dakatar da yaƙin da ke tsakaninsu tare da komawa teburin tattaunawa domin gyara yarjejeniyar da aka cimma a watan da ya gabata.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Pakistan, Tahir Andrabi ya ce duk da ƙalubalen da aka samu wajen aiki da yarjejeniyar, Pakistan za ta ci gaba da ƙarfafa ɓangarorin biyu don kawo ƙarshen rikicin.

    ''Muna fatan halin da ake ciki kan mashigar Hormuz zai daidaita nan ba da jimawa ba''.

    Ya ƙara jaddada muhimmancin mashigar tare da ci gaba da tsareta da samar da ƴancin walwala ga jiragen da ke bi da wurin.

    A wannan makon ne Amurka da ƙaddamar da hare-hare kan Iran, yayin da ita ma tehran ta mayar da martani wajen kai wa sansanonin sojin Amurka hare-hare a yankin Gulf.

  15. 'An kashe wani babban injiniya Zaporizhzhia'

    Kamfanin makamashin nukiliya na gwamnatin Rasha ya ce an kashe babban injiniyan tashar samar da wutar lantarki ta nukiliya a yankin Zaporizhzhia, da ke Ukraine, wadda Rasha ke iko da ita, a harin da wani jirgin mara matuƙi na ƙasar Ukraine ya kai kusa da tashar.

    Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta ce an sanar da ita game da mutuwar jami'in, tare da sake nanata kiranta da a dakatar da duk wani hari da ake kai wa kusa da cibiyoyin nukiliya da ma'aikatansu.

    Sojojin Rasha sun ƙwace iko da tashar Zapo-rijiya ne a makonnin farko na mamayar da Moscow ta ƙaddamar kan Ukraine a shekarar 2022.

    A wani labarin kuma, Rasha ta sake kai wa Kyiv babban birnin Ukraine, hare-haren makamai masu linzami , inda aka ba da rahoton fashe-fashe da dama a safiyar yau Alhamis.

  16. An ji ƙarar sabbin fashewa a Iran

    An ji ƙarar fashewar abubuwa a sassa daban-daban na Iran, ciki har da yankunan da ke nesa da Tekun Fasha, yayin da rundunar sojin Amurka ta sanar cewa ta ƙaddamar da wani sabon zagayen hare-hare.

    A babban birnin ƙasar, Tehran, an yi amfani da na'urar kakkaɓo makamai masu linzami yayin da a birnin Ah-vaz da ke kusa da arewacin Tekun Fasha.

    Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ce an kwashe marasa lafiya daga wani asibiti saboda hare-haren makamai masu linzami da aka kai a kusa da yankin.

    Babban mai shiga tsakani na Iran a tattaunawarta da Amurka, Mohammed Bagher Qalibaf, ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa ƙasarsa na ci gaba da bin tafarkin tattaunawa da kuma yaƙi a lokaci guda, amma ya zama dole Iran ta ci gaba da riƙe ikon kula da mashigin ruwan Hormuz.

    Iran ta mayar da martani tana mai cewa ta mayar da hankali ne wajen lalata cibiyoyin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokacin domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muek wallafawa