Kotu ta bayar da umarnin ƙwace kadarori fiye da 40 masu alaƙa da Malami
Alƙaliyar babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya ta bayar da umarnin wace kadarori fiye da 40 masu alaƙa da tsohon ministan shari'ar ƙasar, Abubakar Malami.
Maishari'a Joyce Abdulmalik ta bai wa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci damar ƙwace kadarorin saboda wanda ake zargin ya kasa zuwa gaban kotun domin kare kansa kan ko ya mallaki kadarorin da halastacciyar hanya.
Kafin bayar da hukuncin alƙaliyar ta yi watsi da wasu kiraye-kiraye da ƴan'uwan Malami da wasu kamfanoni masu alaƙa da kadarorin inda suke ikirarin mallakar kadarorin.
Maishari'a Joyce ta ce abin da ke gaban kotu ba ''batun wanda ya mallaki kadarori ba ne, magana ce ta hanyar da aka bi wajen mallakarsu''.
A cewarta wanda ake kara ya kasa gamsar da kotu cewa an mallake su ne ta halastacciyar hanya.