Barca za ta dauke wa Arsenal Hincapie, Man U da Chelsea na neman Scott

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Barcelona na nazarin yiwuwar daukar dan wasan baya na Arsenal kuma dan ƙasar Ecuador, Piero Hincapie mai shekara 24. (Mail)

Dan wasan baya na Manchester City kuma dan ƙasar Portugal, Ruben Dias mai shekara 29, ya umarci wakilansa su fara duba yiwuwar barinsa kungiyar, inda Paris Saint-Germain da Bayern Munich da kuma Real Madrid ke sa ido kan halin da yake ciki. (Caught Offside)

Liverpool na kokarin cimma yarjejeniya cikin gaggawa da dan wasan gefe na RB Leipzig, Yan Diomande, yayin da Paris Saint-Germain da Manchester City suka fara tattaunawa da dan wasan na Ivory Coast mai shekara 19. (Florian Plettenberg)

Crystal Palace na son shawo kan dan wasan tsakiyar Ingila Adam Wharton mai shekara 22 da kuma dan wasan Japan Daichi Kamada mai shekara 29 su ci gaba da zama a kungiyar bayan nasarar da suka samu a wasan karshe na Conference League. (Sky Sports)

Bournemouth na kokarin dakile duk wani tayi a bazara kan matashin dan wasan gaba na Faransa Eli Junior Kroupi mai shekara 19, da dan wasan gefe na Brazil Rayan mai shekara 19, da kuma dan wasan tsakiyar Ingila Alex Scott mai shekara 22, saboda yadda kungiyoyi da dama ke nuna sha'awa a kansu. (Guardian)

Manchester United da Chelsea na daga cikin kungiyoyin da ke tunanin zawarcin Alex Scott a kasuwar musayar 'yan wasa ta bazara. (Teamtalk)

Dan wasan gaba na Jamus Niclas Fullkrug mai shekara 33 na son barin West Ham United, inda Werder Bremen ke cikin kungiyoyin da ke sha'awar daukarsa. (Sky Germany)

Kungiyar Portugal ta Sporting na son sake daukar dan wasan tsakiyar Portugal Joao Palhinha mai shekara 30 bayan karewar zaman aro da ya yi a Tottenham daga Bayern Munich. (A Bola)

Leeds United na shirin zawarcin dan wasan tsakiyar Lyon kuma dan Amurka Tanner Tessmann mai shekara 24 a wani bangare na harkokin saye da sayarwa da kungiyar ke shirin yi a bazara. (Football Insider)

Manchester City na nazarin matakin da za ta dauka idan dan wasan gefe na Brazil Savinho mai shekara 22, wanda Tottenham ke sha'awar dauka, ya bar kungiyar. (Fabrizio Romano)