Spurs na son ɗaukar Savinho, United na son Anderson

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tottenham sun shiga mataki na gaba kan siyen ɗan wasan Manchester City Savinho kan fam miliyan 60. (Mail)

Manchester United ta dage wajen ɗaukar ɗan wasa Elliot Anderson, inda shugabanin ƙungiyar ke ci gaba da bayana ƙwarin guiwar su na doke Manchester City , wajen ɗaukar ɗan wasan da Nottingham Forest ta yi masa farashi na Fam miliyan 100. (Guardian)

Anderson na son komawa Manchester City, maimakon Manchester United. (Talksport)

Atletico Madrid da Barcelona na ci gaba da gwada ƙwanji wajen ɗaukar ɗan wasan Chealse Marc Cucurella, yayin da dan wasan ke son sauya ƙungiya bayan shafe tsawon shekaru 4 a Stamford Bridge. (Marca - in Spanish)

Newcastle za ta hari dan wasan Monaco Lamine Camara, idan har Sandro Tolani ko Englishman Joe Wilock suka yanke shawarar barin St James' Park a wannan kaka.(Telegraph - subscription required)

Manchester United na ci gaba da sa ido kan ɗan wasan Inter Milan Pio Esposito, a wasan da Italiya za ta buga na sada zumunta da Greece (Teamtalk)

Ɗan wasan Paris St-Germain Randal Kolo Muani, who spent last season on loan at Tottenham, wants to join Juventus where he had a six-month loan spell in 2025. (Tuttosport - in Italian)

Manchester City na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Real Madrid Rodrygo, da dan wasan Everton Iliman Ndiaye. (Mail)

Ɗan wasan bayan Portugal Gancalo Inacio da ke taka leda a Sporting, na cikin jerin ƴan wasan da Liverpool ke son ɗauka bayan dan wasan bayan su Ibrahima Konate. (Caughtoffside)

Atalanta na tattaunawa da Nottingham Forest wajen ganin sun sami nasarar ɗaukar ɗan wasan bayan Italiya Nicolo Savona, komawa Serie A. (Goal - in Italian)

AC Milan ta shira shiga tattaunawa zagaye na biyu kan dauko tsohon mai horar da Crystal Palace Oliver Glasaner, don ganin ya zama kociyan ƙungiyar. (Calciomercato - in Italian)