Mutanen da bai kamata su sha mangwaro ba

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A lokacin zafi a Najeriya, mangwaro na daga cikin ƴaƴan itatuwa da ke jan hankalin mutane sosai.

Laushinsa da zaƙinsa, da ƙamshinsa suna sa mutane da dama su kasa rabuwa da shi.

Amma duk da wannan farin jini na wannan ƴaƴan itatuwa, masana lafiya sun ce ba kowa ne ya kamata ya sha ko ya yawaita shan mangwaro ba.

A wasu lokuta, abin da ake ɗauka a matsayin "kyakkyawan abinci mai gina jiki" na iya jawo matsala ga wasu rukunin mutane idan ba a yi hankali ba kamar yadda wata ƙwararriya a harkar abinci, Dr. Amina Yusuf ta bayyana wa BBC.

Waɗanne sinadarai ne a cikin mangwaro?

Ƙwararriyar ta ce mangwaro na ɗauke da sinadarai da dama masu amfani da ƙara wa jiki kuzari da kariya daga wasu cututtuka.

Sinadaran da ke cikin mangwaro sun haɗa da:

  • Sinadarin vitamin C da ke taimakawa wajen ƙarfafa garkuwar jiki da kuma gyaran ƙwayoyin halitta.
  • SinadarinVitamin A (beta-carotene): Wannan sinadarin yana da amfani ga ido da lafiyar fata.
  • Sinadarin Fiber - Ta ce wannan yana taimakawa wajen narkar da abinci da rage kumburin ciki.
  • Sinadarin Potassium - Wannan yana taimakawa wajen daidaita bugun zuciya da hawan jini.
  • Sinadarin Folate (Vitamin B9) - Ƙwararriyar ta ce wannan yana da muhimmanci musamman ga mata masu juna biyu.
  • Sinadarin Magnesium – yana taimakawa aikin tsokoki da jijiyoyi in ji ƙwararriyar.
  • Antioxidants kamar Mangiferin da Quercetin da Catechins da Gallic acid suna taimakawa wajen kare ƙwayoyin jiki daga lalacewa.

A cewarta, waɗannan sinadarai na taimakawa wajen kare garkuwar jiki sosai

Wane ne bai kamata ya sha mangwaro ba?

Likitar ta ce duk da waɗannan fa'idodi da mangwaro ke bayarwa ga ɗan'adam, akwai wasu rukunin mutane da ya kamata su yi taka-tsantsan wajen shan shi ko kuma bai kamata su sha ba kwata-kwata.

Mutanen sun haɗa da;

Masu ciwon suga

Mangwaro na ɗauke da sukari duk da cewa ba irin sukarin cikin kayan zaki ba ne, yawan shan mangwaro na iya haifar da tashin matakin sikarin jini.

"Ba zan ce mutanen da ke fama da ciwon sukari ka da su sha mangwaro kwata-kwata ba, amma ya kamata su kula da adadin da suke sha. Yawan shan sa a lokaci guda na iya shafar yadda jiki ke sarrafa sukari," in ji Dr Amina.

Masu fama da matsalar ƙoda

Ƙwararriyar ta ce sinadarin Potassium na daga cikin sinadarai masu yawa a mangwaro. Duk da cewa potassium yana taimakawa wajen sarrafa bugun zuciya da aikin tsokoki, mutanen da ƙodarsu ba ta aiki yadda ya kamata za su iya fuskantar matsala idan suka sha.

Idan potassium ya yi yawa a jiki, zai iya haifar da matsalolin bugun zuciya da sauran matsaloli masu tsanani.

Masu fama da matsalar ƙanjiki

Ko da yake ba kasafai ake samun hakan ba, akwai mutanen da jikinsu ke nuna rashin jituwa da mangwaro in ji ta.

"Masu irin wannan matsalar sukan ji ƙaiƙayin baki ko maƙogwaro ko ƙuraje a fata ko

Kumburin leɓɓa ko su samu matsalar numfashi a wasu lokuta idan suka sha mangwaro."

Masu fama da gudawa ko matsalar hanji

Mangwaro na ɗauke da dussa, wato 'fiber' mai yawa wanda ke taimakawa wajen motsa hanji.

Sai dai ga mutanen da ke fama da gudawa ko wata matsalar hanji, yawan cin mangwaro na iya ƙara tsananta matsalar.

Mutanen da ke son rage nauyi ko ƙiba

Ko da yake mangwaro na da amfani ga lafiyar jiki, yana ɗauke da adadin kuzari da sukari fiye da wasu ƴaƴan itatuwa, in ji ta.

"Mutanen da ke son rage nauyi ko ƙiba bai kamata su sha mangwaro ba ko kuma ya kamata su rage shan shi sosai.

Yadda ya kamata a sha mangwaro

Ƙwararriyar ta ce mangwaro na da amfani ga lafiyar jiki idan aka sha shi cikin daidaitaccen adadi.

Ta lissafo hanyoyin da suka kamata a bi wajen shan mangwaro kamar haka;

  • A zaɓi mangwaro mai kyau da ya nuna: Ƙwararriyar ta ce ya kamata a sha mangwaron da ya nuna sosai kuma guda ɗaya ko kuma yanka kaɗan a rana na iya wadatarwa a matsayin wani ɓangare na abinci mai gina jiki.
  • A wanke shi sosai kafin a ci
  • A guji yawan shan mangwaro a lokaci ɗaya
  • A sha shi bayan cin wani abinci mai gina jiki
  • A guji cin ɓawon mangwaro ga wasu mutane