Tottenham na son Savinho, Milan na harin Phil Foden

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tottenham na da ƙarfin guiwar son ɗaukar ɗan wasan Manchester City da Brazil Savinho. (Fabrizio Romano)

Real Madrid ba ta da wani shiri na ɗaukar ɗan wasan Manchester City, Rodri a wannan kaka. (Athletic - subscription required)

AC Mila na ci gaba da tuntuɓar dan wasan Ingila da Manchester City. (Tuttosport).

Sai dai suna dukkan wata buƙata ta son daukar Foden, za ta tabbata ne idan AC Milan ta iya siyar da dan wasan Portugal Rafael Leao. (Tuttosport)

Mai tsaron bayan Leicester City Ben Nelsonya sanar da ƙungiyar cewar zai bar su, yayin da Manchester United da West Ham.(Mail)

Arsenal sun shirya ɗaukar dan wsan bayan Ingila Elijah bayand a dan wasan ya ƙi amincewa da sabunta kwantaraginsa da Tottenham. (Fabrizio Romano)

Ana sa ran ɗan wasan Portugal Joao Palhinha zai koma Bayern Munich lokacin da zaa fara wasanin tunkarar wasanni gaba, yayin da ake cewar Aston Villa na son ɗaukar ɗan wasan. (Sky Germany)

Liverpool ta kamala shirye shiryen ɗaukar ɗan wasan Colombia Samuel Martinez daga Atletico Nacional Fam dubu dari bakwai da hamsin. (Athletic - subscription required)

Real Madrid, da Barcelona, da Atlentico Madrid na son ɗaukar Tottenham da Arjantina Cristian Romero. (Teamtalk)

Juventus sun shiga Borrussia Dortmund da Surderland a yunƙurinsu na daukar dan wasan Amurka Folarin Balogun daga Monaco. (Mundo Deportivo)

Har yanzu Chelsea na ci gaba da tattunawada dan wasan bayan Faransa Maxence Lacroix, sai dai Crystal Palace na neman fam miliyan 70, wanda shi ne ke kawo tsaiko siyen ɗan wasan. (Caught Offside)

Har Juventus na son Tottenham da Brazil Richarlison. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Everton ta fi sauran ƙungiyoyin damar iya ɗaukar ɗan wasan Ingila, Jaden Philogene daga Ipswich.(Football Insider)